Ban mayar da martani kan batun hidimar ƙasata ba – Musawa

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ministar Fasaha, Al’adu da Tattalin Arziki, Hannatu Musa Musawa ta ƙaryata labaran da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na zamani da ma wasu jaridun ƙasar nan dangane da tirka-tirkar da ta mamaye batun hidimar ƙasarta, wato NYSC.

Batun ya samo asali ne tun bayan da wata ƙungiyar marubutan kare haƙƙin ɗan’adam wato YURIWA, ta fitar da ƙorafi a kan ministar cewa ba ta kammala hidimar ƙasa ba ta shekara ɗaya wanda doka ta wajabta wa kowane ɗan Nijeriya bayan ya kammala karatun jami’a.

Fitar wannan labari ke da wuya sai d’Daraktan hulɗa da jama’a na hukumar da ke kula da hidimtawa ƙasa, Eddy Megwa, ya tabbatar da ƙorafin da ƙungiyar ke yi a kan ministar.

Daraktan ya bayyana cewar riƙon muƙamin minista da Musawa ke yi a halin yanzu ya saɓa wa dokar hukumar ta NYSC.

Ya ci gaba da cewa, karɓar wani muƙamin gwamnati ga wanda ke hidimar ƙasa saɓa wa dokar hukumar ne, har sai ya kammala NYSC ɗin na tsawon shekara ɗaya.

Ya ce Musawa ta fara hidimar ƙasarta a shekarar 2001 a jihar Ebonyi, inda daga baya ta koma jihar Kaduna don ci gaba da hidimar ƙasar.

Sai dai a lokacin da ta koma Kadunar, ta gudu ta watsar da hidimar ƙasar ba ta kammala ba, hakan kuma zai iya sa hukumar ta ɗauki mataki a kanta.

Sai dai a wani labarin da ya karaɗe kafafen yaɗa labarai, rahotanni sun ambato ministar tana cewa ba ta karya dokar ƙasa ba, duk da a cikin takardar dake yawo Musawa ta tabbatar cewa yanzu ne take hidimar ƙasar a birnin Abuja, inda ta amince cewar ba ta samu zarafin kammala hidimar ƙasar ba wanda ta fara a shekarar 2001 sakamakon wani lamari na iyali.

Wannan dalili ne yasa ta sake yin rajista da hukumar ta NYSC domin kammala hidimta wa ƙasar, wanda a halin yanzu tana cikin wata na 8 da farawa kafin shugaba Tinubu ya naɗa ta a muƙamin minista.

Sai dai da yammacin ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, 2023, ta bakin mataimakin Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar yaɗa labarai ta ƙasa, Suleiman Haruna, Ministar ta fitar da wata takarda da aka raba wa manema labarai inda Musawa ke musanta cewar bata mayar da martani ba dangane da batun na hidimar ƙasarta kamar yadda ake yaɗawa.

“An ja hankalin Ministar Fasaha al’adu da tattalin arziƙi dangane da wata takarda mai taken ‘martani na a kan batun hidimar ƙasa a matsayina na minista.’

Ya ce an danganta ministar a kan batun NYSC ba yadda ya dace ba.

“Ministar tana sanar da cewa ita ba ta fitar da wata takarda ba a hukumance dangane da lamarin don haka ne ta buƙaci al’uma a kan su dinga taka-tsan-tsan a kan labarin da ba a tantance ba.” Inji Sanarwar.

Daga ƙarshe, Ministar ta yi godiya dangane da goyon baya, amanna da fahimtar ta da ‘yan Nijeriya suka yi a kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *