Ban taɓa rubutu don kuɗi ba – Jidda Washa

“Kare martabar mata da yaƙi da fyaɗe ya sa na fara rubutu”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ɗaya daga cikin matasan marubuta da tauraruwar su ke haske cikin jerin marubuta mata da ke sakin rubuce rubucen su a kafafen sada zumunta na ‘online’, Malama Jidda Washa, wacce ta rubuta littattafai da gajerun labarai da dama da ke ɗauke da darussa daban daban na kyautata rayuwa. A tattaunawar ta da Manhaja, marubuciyar ta bayyana abin da ya fara zaburar da ita ta fara rubutu, da burin ta a harkar adabi.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kan ki?
JIDDA: Sunana Hauwa’u Adam Suleiman wacce aka fi sani da Jidda Washa. Ni asalin ‘yar Jihar Kano ce, amma an haife ni ne a Jihar Ribas, a shekara ta 1997. Na yi karatuna daga firamare zuwa Diploma a ɓangaren ilimin gudanarwa, sannan na yi NCE a ɓangaren ilimin Turanci da Tattalin Kuɗi, sannan na samu nasarar sauke karatun Alƙur’ani mai girma da haddar izu ashirin da uku.

Ko za ki gaya mana yadda ki fara sha’awar harkar rubutu?
Na fara sha’awar rubutu ne sakamakon yadda na lura wasu varagurbin mutane suna cin zarafin ‘ya’ya mata, da amfani da raunin da suke da shi ko ƙarancin wayewa suna sa rayuwar su cikin wata rayuwa marar tsafta, da ba ta dace da mutunci da martabar ‘ya mace ba. Musamman a ‘yan shekarun baya, lokacin da aka samu yawaitar aikata fyaɗe, kan ƙananan yara da ‘yan mata da ba su riƙa ba.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai nawa, kuma an buga su ne ko a yanar gizo kawai kike fitar da su?
Na rubuta littafai bakwai, kuma dukka a yanar gizo na ke sakin su. Akwai labarin, ‘In ka ƙi ji’, akwai ‘Rayayye daga matacce’, ‘Mutuwar kasko’, ‘Tarnaƙi’, sai ‘Baƙar inuwa’ da kuma ‘Butulcin so’. 

Wane saƙo kika fi mayar da hankali a kai cikin rubuce rubucen ki?
Na fi mayar da hankalina a kan rubuce rubucen da suka shafi faɗakarwa, ƙalubalen rayuwa da harkokin yau da kullum da siyasa.

Yaya ki ke samun fasahar yin rubuce rubucen ki, ko akwai wani da yake koya miki rubutu?
Ni bani da wani wanda yake koya min rubutu ko sa min ra’ayin abin da zan yi rubutu a kai, baiwa ce kawai daga Allah. Idan na yi tunanin mai zan rubuta, sai kawai na nemi taimakon Allah.

Yaya ki ka ga tasirin rubutun adabi da ake sakewa a yanar gizo a maimakon a littafi na takarda da ake bugawa?
Tsarin rubutun adabi da ake sakewa a yanar gizo, ba laifi ba ne, a na wa hasahen tun da kowa da abin da ya fi masa sauqi, kuma dama ai an ce shan koko ɗaukar rai ne. Kuma babu shakka rubutun na samun tasiri sosai a wajen masu karatu. Yanzu haka a kashi ɗari an samu sauyi mafi yawa wanda zai kai kashi tamanin na shiryuwar yara da matasa, sanadiyyar rubuce rubuce na ‘online’ masu saurin isa ga jama’a.

Ka san yanzu zamani ya juya, da yawa mutane sun fi ta’allaƙa a kan kafafen sadarwa na zamani, a maimakon littafi. Kuma ai dama muhimmin dalilin yin rubutu shi ne isar da saƙon faɗakarwa ga al’umma. 

Wasu marubutan ‘online’ irin ki kan buɗe zaure na musamman a manhajar WhatsApp ko Facebook, dangane da wani labarin da suka rubuta, don jin ra’ayoyin masu karatun rubuce rubucensu. Yaya alaƙar ki da masu karatun littattafanki?
Sam, ni ban taɓa sha’awar buɗe shafin zaure na wa na ƙashin kaina ba. Kawai idan na yi rubutu na fitar shi kenan, ba na bibiya. Amma ina yawan samun saƙonnin fatan alheri ta akwatin sirrina na whatsapp. 

Batun samun wani kuɗin shiga ta dalilin rubuce rubucen ki fa, Wacce hanya kike bi don ganin kin ci guminki a harkar rubutu?
Ban taɓa rubutu don kuɗi ba, ko don samun kuɗin shiga ba. Ni ‘yar kasuwa ce, daidai gwargwado ina samun abin ɓatarwa wanda zan yi buƙatuna na yau da kullum, har ma na yi wa wasu.

Kin shiga gasar marubuta kamar guda nawa, kuma wacce nasara kika samu?
Na shiga gasannin marubuta kamar guda huɗu. Gasar marubuta ta ƙungiyar POWA, gasar Ɗangiwa, gasar Hikayata ta BBC da kuma gasar marubuta matasa mata zalla ta wannan shekara. Na samu nasara a gasar POWA inda na zo ta biyu. Na samu nasara a gasar Ɗangiwa. Sannan kuma ragowar gasannin biyu a wannan shekarar na shiga, ban san abin da Allah zai yi ba. Amma ina yi wa kaina da ragowar matan da suka shiga fatan nasara.

Ki na ganin irin waɗannan gasar marubuta da wasu kamfanoni, ko kafafen watsa labarai da ƙungiyoyi ke shiryawa zai kawo wani sauyi a harkar rubuce-rubuce?
Tabbas zai kawo sauye-sauye masu yawa da kuma fa’idantuwa. Kuma hakan na sake fitar da tauraro don a san shi a kuma san kaifin alƙalamin shi. Saboda haka ina ganin babban cigaba ne shirya gasar marubuta ke haifarwa ga rayuwar marubuci ko marubuciya. 

Mene ne ra’ayinki game da yadda za a bunƙasa harkar rubuce rubuce, ta yadda marubuta za su samu kima da martaba a idon jama’a da gwamnati?
Ra’ayina bai wuce gwamnati ta san da matsayin marubuta ba, ya kasance akwai wani taimako da za ta riƙa ware wa harkar rubuce-rubuce da kuma qimanta marubuci da marubuciya. Sannan kuma gwamnati ta bayyana marubuci a matsayin mariƙin rayuwa, wato tauraron al’umma. Wannan shi zai sa mutane su girmama alƙalami da ma’abota alƙalami da gangar jikinsu.

Wacce nasara ko cigaba ki ka taɓa samu ta dalilin rubutu, da ya ƙara mi ki ƙwarin gwiwa?
Na samu nasarori da ba zan iya iyakance su ba, kuma har yanzu ina kan ci gaba da samun nasarori, da suka haɗa da ɗaukaka, kyaututtuka daga masoya da dai sauransu.

Bangon ɗaya daga cikin litattafan da Jidda Washa ta rubuta

Wane fata ki ke da shi nan gaba a rayuwarki, a matsayinki ta marubuciya?
Ina fatan nan gaba in zama shahararriyar marubuciya kuma dattijuwar marubuta. Ina kuma da burin nan gaba in ga ana damawa da marubuta a kan sabgogi na siyasa, tallace tallacen kamfanoni da dai sauran manyan harkokin cigaban al’umma. 

Wacce shawara za ki bai wa sabbin marubuta da masu sha’awar shiga harkar rubutu?
Shawarata ga sababbin marubuta, su sani idan za su yi rubutu, su kasance masu bincike da neman sani a kan rubutun da za su yi, domin rubutun su ya zama mai inganci kuma karɓaɓɓe a wajen jama’a. 

Wabe karin maganar Hausa ce ke tasiri a rayuwarki?
‘Idan ɓera da sata, to daudawa ma na da wari’.

Mu na godiya, Hajiya Jidda. 
Ni ma Ina godiya, Blueprint Manhaja.