Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya mayar da martani ga tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), wanda ya ce ya roƙi marigayi Janar Sani Abacha kada ya kashe shi. Obasanjo ya kasance cikin waɗanda aka kulle a lokacin mulkin Abacha kan zargin yunƙurin juyin mulki.
Da yake magana a bikin Kirsimeti na haɗin kai na Plateau Interdenominational Unity Christmas Carols da Praise Festival da aka gudanar a Dandalin Addu’a na Umarni Goma a Du, Jos ta Kudu, a ƙarshen mako, Gowon ya bayyana cewa ya rubuta wa Abacha wasiƙa, yana masa nasiha cewa Allah ya ba shi mulki ne domin yin alheri, ba sharri ba, tare da roƙon a sassauta wa Obasanjo. Ya ce ya aika da wasiƙar ne ta hannun matarsa zuwa Abuja da dare, wanda hakan ya kawo sauyi a lamarin.
Da yake maida martani a ranar da ta biyo bayan jawabin Gowon a wajen bikin, Obasanjo ya bayyana cewa bai san Gowon ya yi irin wannan kokari ba sai da ya ji daga bakinsa. Ya ce bayan an sake shi daga gidan yari, ya yi yawo a cikin gida da wajen Ƙasar domin nuna godiya ga waɗanda suka taimaka wajen roƙon sakin sa. Ya kuma bayyana farin cikin sa da kuma gode wa Gowon kan matakin da ya ɗauka.
A jawabinsa, Obasanjo ya ce: “Ina son godewa shugaban nawa, Janar Yakubu Gowon. Jiya ya bayyana wani abu da ban sani ba sai yanzu. Bayan na fito daga kurkuku, na gode wa abokai na a ciki da wajen Ƙasar nan da suka yi addu’o’i da roƙo a kan sakin nawa. Amma ban san cewa ka rubuta wasiƙa ta musamman ba sai jiya da ka bayyana hakan,na gode maka kan haka.”
A yayin taron, Obasanjo ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang bisa ƙoƙarin sa na inganta zaman lafiya da ci gaba, tare da yi masa fatan alheri a ayyukan da ke gaba.