Banka wa ofis ɗin mu wuta a Inugu koma-baya ne, inji INEC

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana gobarar da aka yi a ofishin ta na Ƙaramar Hukumar Udenu da ke Jihar Inugu a matsayin wani sabon koma-baya a tsare-tsaren da ta ke yi na shirya zaɓuɓɓukan da ke tafe nan gaba.

Hukumar ta faɗi haka ne a cikin wata sanarwa da Mista Festus Okoye, Babban Kwamishinan ta mai kula da Yaɗa Labarai da Wayar da kan Masu Zaɓe, ya raba a ranar Juma’a.

Okoye ya bayyana damuwa kan yadda yawan ƙona kayan hukumar a wasu jihohi ta hanyar gobara ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Ya ce, “Yanzu kuma a Jihar Inugu abin ya faru, inda Zaunannen Kwamishinan Zaɓe na jihar, Mista Emeka Ononamadu, ya kawo rahoton cewa an banka wa ofishin INEC na Ƙaramar Hukumar Udenu wuta.”

Ya ce abin baƙin cikin da ya faru ɗin ya auku ne wajen kimanin ƙarfe 8:40 na dare a ranar Alhamis, amma ba a samu salwantar rai ba.

Amma, a cewar Okoye, an yi matuƙar lalata ginin ofishin, kuma kayan zaɓe da na aikin ofis duk sun ƙone duk da ƙoƙarin da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Inugu ta yi wajen kashe gobarar.

Ya ce INEC ta ji daɗin ƙoƙarin da hukumar ‘yan kwana-kwanan ta yi.

Okoye ya ce an sanar da ‘yan sanda abin da ya faru domin su yi bincike.

Ya ce, “Wannan shi ne karo na uku da ake sanya wa ofisoshin INEC wuta a ƙananan hukumomi da ke jihohi uku a cikin ƙasa da mako biyu.

“Na farko, an lalata ofis ɗin mu na Ƙaramar Hukumar Essien Udim da ke Jihar Akwa Ibom a ranar 2 ga watan Mayu.

“Daga nan sai wutar da ta tashi a ofishin mu da ke Ƙaramar Hukumar Ohafia na Jihar Abiya a ranar 9 ga Mayu.

“Wannan wani ƙarin koma-baya ne ga ayyukan da hukumar ke yi da shirye-shiryen ta na zaɓuɓɓukan da ke tafe.”

Okoye ya tuno da cewa bayan harin da aka kai a Abiya, hukumar ta yanke shawarar ta kira wani taron gaggawa na kwamitin tuntuɓar hukumomin tsaro kan zaɓe, wato ‘Inter-Agency Consultative Committee on Election Security’ (ICCES) a makon gobe domin tattauna wannan abin damuwar wanda ke faruwa.

Ya ce lalata gini da kayan aikin hukumar da ya faru a yanzu a Jihar Inugu ya na buƙatar a yi saurin duba matakan da su ka kamata don tsare kayan INEC a dukkan jihohin ƙasar nan.

“Saboda haka, hukumar za ta kira taron gaggawa na dukkan zaunannun kwamishinonin ta, wato ‘Resident Electoral Commissioners’ (RECs) a ranar Laraba, 19 ga Mayu, a Abuja kafin taron kwamitin na ICCES.”

Sai dai babban kwamishinan ya bayyana ƙudirin hukumar na ci gaba da aiwatar da ayyukan da aka ɗora mata, cikin su har da kammala aikin ƙara yawan rumfunan zaɓe.

Sauran, a cewar sa, sun haɗa da ci gaba da rajistar masu zaɓe (CVR), da ayyukan ƙara wa ma’aikata ƙarfin aiki, da sake duban fasalin Babban Tsarin Aiki (Strategic Plan) na 2022-2026, da ƙarfafa hulɗa da masu ruwa da tsaki da kuma gudanar da dukkan zaɓuɓɓukan da aka tsara za a yi.

A wani labarin mai alaƙa da wannan, an ruwaito Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Inugu, Mista Mohammed Aliyu, ya bada umarnin a binciki gobarar da aka yi a ofishin INEC da ke Obollo-Afor.

Aliyu ya kuma ce a killace wurin don a samu damar gudanar da bincike don tabbatar da hakikanin abin da ya auku tare da gano irin asarar da aka yi.

Kakakin ‘yan sanda na jihar, ASP Daniel Ndukwe, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa ga manema labarai a ranar Juma’a.

Ndukwe ya ce gobarar, wadda ta faru a ofishin INECA da ke Obollo-Afor da ke cikin Yankin Ƙaramar Hukumar Udenu na Jihar Inugu, ta faru ne a ranar 13 ga Mayu, da misalin ƙarfe 9:40 na dare.

Ya ce, “Rundunar ‘yan sanda ta samu kiran koke daga babban ofishin ta na yanki da ke Udenu cewa akwai gobara da ta tashi a ofishin INEC da ke Obollo-Afor a Ƙaramar Hukumar Udenu.

“Nan take jami’an ‘yan sanda da ke aiki a ofishin yankin su ka garzaya zuwa wajen, yayin da su ka kira Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Inugu su ka je wurin su ka kashe wutar ba tare da ɓata lokaci ba.”

Ya ce an kashe wutar kafin ta yaɗu zuwa sauran ofisoshi da ke kusa da ginin, ta hanyar haɗin gwiwar hukumar ‘yan kwana-kwanan da ‘yan sanda da kuma jama’a da su ka taimaka.

Ya c