Bankin Access zai haɗe reshensa na ƙasar Zambiya da African Banking Corporation

Daga AMINA YUSUF ALI

A halin yanzu dai Bankin Access yana shirin haɗe reshenta na ƙasar  Zambiya da wani sabon bankin da ya mallaka watanni tara da suka wuce a can ƙasar Zambiya. Wato African  Banking Corporation, Zambiya.

Bankin access shi ne bankin da ya fi kowanne banki a ƙasar nan ƙarfin kadara. Kuma ya samu damar mallakar wancan rukunin bankin na Zambiya watanni tara da suka gabata. 

Wannan haɗakar kamar yadda jaridar premiumtimes ta rawaito, za ta ƙara haɓaka yawan bankunan Access ɗin a ƙasar Afirka ta Kudu har zuwa rassa guda 70 a ƙasar. Sannan zai ƙara wa bankin abokan hulɗa har zuwa dubu ɗari uku (300,000), da kuma ƙarfin kadarar bankin har zuwa dalar Amurka biliyan guda.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin wani saƙo da Bankin Access fin ya aike wa Hukumar canjin kuɗi ta Nijera a ranar Litinin ɗin nan da ta gabata.

Da ma bankin yana ta shirye-shiryen ƙara bunƙasa inda yake harin manyan ƙasashe a Afirka ta Kudu kamar, Muzambik,  Afirka ta Kudu, Zambiya da kuma Botswana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *