Bankin CBN: Jagorancin Emiefele ya durƙusar da tattalin arzikin ƙasa – Kakakin Majalisar Matasan Arewa

An bayyana cewa muddin ba a yi abin da ya kamata ba a kan lokaci, Nijeriya za ta faɗa cikin wani mawuyacin hali ta dalilin shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emiefele.

Kakakin Majalisar Matasan Nijeriya, Mohammed Salihu Danlami shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Litinin.

Ɗanlami ya ce, Godwin Emiefele shi ne mafi munin abin da ya taɓa faruwa ga Nijeriya da tattalin arzikin ta, duba da yadda sha’anin tattalin arzikin Nijeriya ke fuskantar koma-baya, musamman yadda darajar kuɗin ƙasar ke ta ja baya.

Ya ce Emiefele mutum ne mai fuska biyu, ɗaya na tare da gwamnati, yayin da gudan na da burin zama shugaban ƙasa. Tare da cewa harkokin talikin sun jefa ƙasar nan cikin ƙarin taɓarbarewar tattalin arziƙin Nijeriya.

A matsayinsa na shugaban CBN, “Mista Godwin Emiefele ya taka rawar gani sosai wurin durƙusar da tattalin arzikiƙin Nijeriya tun bayan da ya zama Gwamnan Babban Bakin wanda kafin zuwansa aka ce CBN yana ɗaya daga cikin masu saurin bunƙasa a duniya.

“Amma a yau CBN ya zama abin tausayi idan aka kwatanta shi da ƙaramar ƙasa da ke da raunin tattalin arziƙi a Afirka, za ku yarda da ni cewa kafin Mista Emiefele ya karɓi shugabancin bankin, Naira, wacce ita ce kunin mu na mu’amalar musayar kuɗi a kan Dala 1 zuwa N170 amma a yau, ba mu buƙatar a yi mana bayanin cewa darajar Naira ta lalace ainun”, in ji Ɗanlami.

Haka nan, ya ce “Duk wannan ya faru ne saboda rashin ƙwarewarsa a fagen gudanar da bankin CBN wanda ya cika da kwaɗayi, cin hanci da rashawa da rashin manufofi masu kyau, rashin nasarar Mista Emiefele ya wuce tunanin da ake tsammani, amma duk da haka gwamnati ta yi shuru lokacin da ake ta kiraye-kirayen kada Shugaban Ƙasa ya sake naɗa shi a karo na biyu.

“Ayau, tsoron ‘yan Nijeriya da dama yana bayyana kan yadda tattalin arziƙin ƙasar ke saurin durƙushewa da kuma yadda ake samun hauhawar farashin kayayyaki kulli yaumi.”

Ɗanlami ya yi zargin cewa Emiefele da abokan harƙallarsa masu haɗama da ‘yan siyasa sun yi babakere a kan shiryen-shiryen CBN don faɗaɗa aljihunsu da kuma cutar da cigaban ƙasa da walwalar ‘yan ƙasa.

A ƙarshe, Ɗanlami ya ce abin bakin ciki ne da takaici ganin yadda CBN ya zama sabon wurin kashe-mu-raba na wasu ‘yan Majalisar Tarayya.