Bankin Duniya da Hukumar Ƙidaya sun horar da ’yan jarida kan yawan al’umma don inganta rayuwa

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Legas

Bankin Duniya da Hukumar Ƙidaya ta Nijeriya (NPC) sun shirya wa wasu zaɓaɓɓun ’yan jarida horarwa kan kula da yawan al’umma, don inganta rayuwar ’yan Nijeriya.

An shirya horon na kwana uku ne a otel ɗin Lagos Intercontinental da ke Birnin Ikko a ranakun Litinin, 17 zuwa Laraba, 21 ga Yuli, 2022.

A ranar Litinin an fara da gabatar da maƙasudin taron ne, inda shugabannin jami’an Bankin Duniya da na Hukumar NPC suka gabatar da jawabai tare da tattaunawa da mahalarta taron kan alƙiblar da ta kamata ’yan Nijeriya su sanya a gaba kan batun yawan al’umma bisa la’akari da tattalin arzikin ƙasa.

A washegari ranar Talata masana da masu ruwa da tsaki daga fannoni daban-daban na rayuwa suka bajekolin maƙaloli da ƙasidu kan yadda yawan jama’a ke da tasiri ta fuskar tattalin arziki, lafiya, ilimi da sauransu ga al’ummar kowacce ƙasa.

Haka nan ’yan jarida sun samu damar gabatar da tambayoyi daban-daban ga masana da masu ruwa da tsaki, don ƙara samun wayewa kan batun da ake tattaunawa akai.

A ranar Laraba kuwa sai aka bai wa mahalarta taron, wato ’yan jarida, damar samar da sanfurin labarai da rahotanni na musamman na jaridu, talabijin da rediyo, don gwada yadda bitar ta amfanar da su.

A ƙarshen taron dai, an gabatar da waɗannan rahotannin musamman, waɗanda suka ƙayatar matuƙar gaya.