Bankin Keystone ya yaba wa gwamnan Zamfara kan inganta ɗan adam a jihar

Daga BELLO A. BABAJI

Bankin Keystone ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal kan ƙoƙarinsa na inganta rayukan al’umma a Zamfara.

Darakta-Manaja na bankin, Hassan Imam ya jagoranci manyan jami’ansu yayin wata ziyara ga gwamnan a Gidan Gwamnatin jihar dake Gusau.

Cikin wata takarda da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce bankin ya na aikin gyaran makarantun Firamare na Sarkin Kudu da Sakandire na Sambo dake Gusau a matsayin sauƙe nauyin da ke kansu ga al’umma.

A lokacin da ya ke jawabi, Gwamna Lawal ya yaba wa bankin a ƙoƙarinsa na mayar da Zamfara waje da zai dace da yanayi mai kyau ga kasuwanci acikin al’umma.

Gwamna ya ce, su na cigaba da ƙoƙarin ganin an samar da hanya mafi kyau na inganta jihar.

Ya ƙara da cewa, da yardar Allah Zamfara za ta zama mai gogayya da suaran jihohin Nijeriya a kowane ɓangare na ci-gaba.

Dauda Lawal ya ƙara da cewa, nan ba da jimawa ba zai ƙaddamar da makarantun da zarar an kammala gyare-gyaren da ake musu, ya na mai godiya ga bankin ga hoɓɓasar da yayi.

Haka nan, Darakta-Manaja na bankin ya ce nasarorin da Gwamna Lawal ya samu cikin watanni 17 ya kere abin da wasu gwamnoni suka cimma a shekara 20 musamman a harkokin ilimi, lafiya da sauran ababen more rayuwa.

Ya ce, za su cigaba da bai wa gwamnan goyon baya da taimaka masa kan ayyukan bunƙasa harkokin ci-gaba a jihar.