Bankin Standard Chartered zai sake tattara komatsansa daga ƙasashen Afrika bakwai

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai Bankin Standard Chartered ya yi nisa a shirye-shiryensa na tattara komatsansa daga wasu manyan garuruwa 5 da yake cin kasuwar a Afrika. 

Wannan bayani yana ƙunshe a wata sanarwar da Bankin ya yi na cewa zai tattara ya nasa, ya nasa daga wasu ƙasashen Afrika da kuma gabas ta tsakiya. 

A cikin sanarwar da Bankin Standard Chartered ɗin ya saki, ya bayyana ƙasashen Afrika da zai yi adabo da su su ne, Cameroon, Gambiya, Angola, Zimbabwe, Sierra Leone da kuma wasu ƙasashen biyu daga gabas ta tsakiya. Haka wata majiya daga bankin ta bayyana cewa, a yanzu haka ma bankin yana shirin janye harkokin kasuwancisa daga ƙasashen Tanzaniya da Ivory Coast.

Idan mai karatu bai manta ba, a watan Janairun shekarar nan ne Bankin ya sanar da rufe rabin sassan da yake su a Nijeriya. Wato sun kama rassa 13 kenan ya rufe. Sannan a kwanaki ma ya rufe kaso 50 na Rasdan da yake da su a ƙasar Pakistan. 

A ta bakin babban jami’in zartarwa na rukunin bankunan Standard Chartered, Bill Winters, ya bayyana cewa, Bankin ya yanke shawarar haɗa hankalinsa waje ɗaya ya cigaba da harkokinsa a wuraren da suke ganin za su samun cigaba da kuma bunƙasa a harkokin kasuwancinsu. 

Mista Bill Winters, Ya ƙara da cewa, ba wai bankin nasu ba ya samun cigaba ba ne a ƙasashen Afrika ba, amma sun fi sha’awar su ga sun yi harkokinsu a ƙasashen da za su kawo musu bunƙasa da cigaba yadda ya kamata. 

A ƙarshe, ya bayyana irin godiyar da bankin yake yi ga ƙasashen Afrika da irin damar da suka ba su a kan gudanar da  harkokinsu a ƙasashen. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *