Bankin Zenith ne lambawan yanzu a bankunan Nijeriya


An zabi Bankin Zenith a matsayin banki na daya a jerin dukkan bankunan Nijeriya a yau.

Hakan ta faru ne a wajen bikin bada kyaututtuka ga gwarzaye a bangaren aikin banki wanda mujallar The Banker da kamfanonin Finacial Times Group da ke London su ke shiryawa a kowace shekara.

Bikin na bana, wanda aka gudanar a ran Laraba, sunan shi ‘The Banker’s Bank of the Year Awards 2020’.

Da ma tun a farkon wannan shekarar mujallar da guruf din kamfanonin sun zabi bankin na Zenith a matsayin banki mafi daraja a kasar nan a bisa wani sikeli da su ka kafa don auna darajar bankuna.

A wajen zaben gwarzon shekarar, a kan yi la’akari ne da ribar da banki ya samu, da tsare-tsaren da ya fito da su don cimma manufar sa, da kuma yadda ya yi wa kwastomomin sa aiki.

An dauki wannan gasa a matsayin ita ce babban ma’aunin darajar kamfanonin hadahadar kudi a sassa daban-daban na duniya, irin su nahiyar Afrika da yankin Asiya-Pacific, Turai ta Tsakiya da ta Gabas, Latin Amerika, Gabas ta Tsakiya, Arewacin Amurka da Yammacin Turai.

A yayin da ya ke magana kan wannan kyauta da su ka samu, Manajan Daraktan Bankin Zenith, Mista Ebenezer Onyeagwu, ya ce: “Abin farin ciki ne a gare mu a Bankin Zenith a ce mujallar The Banker da Financial Times sun karrama mu da kyautar Gwarzon Banki na shekarar 2020 a Nijeriya.

“Na sadaukar da wannan kyauta ga ma’aikatan mu saboda sadaukarwar su da jajircewar su, kirkiro da sabbin dabaru da kuma kwarewar su.

“A saboda kwarewar ma’aikatan mu ce har bankin ya ci gaba da gina masaniyar sa da iyawar sa da ke kara mana kuzarin inganta kasuwancin mu don ci gaba da yin aiki da babu tamkar sa.”

Mista Onyeagwu ya kuma miƙa godiyar sa ga Shugaban Hukumar Daraktocin bankin, Mista Jim Ovia, saboda rawar da ya taka tun lokacin kafa bankin wajen gina duk wani ginshiki da tsari da ake bukata wajen gina banki mai karfin da za a dade ana damawa da shi, da kuma Hukumar Daraktocin saboda kyakkyawar shawara da jagorancin da su ke bayarwa, da kuma dimbin kwastomomin bankin saboda goyon bayan da su ke bayarwa wanda tabbatar wa da abokan hulda cewa bankin zai iya shiga ko’ina a dama da shi ta kowace fuska.