Daga AMINA YUSUF ALI
Watanni da dama bayan da bankuna sun ƙayyade adadin kuɗin da za a iya cira a ATM a rana guda, yanzu sun ƙara adadin zuwa Naira 200,000. A yanzu haka za a iya cire har Naira 200,000 a kowacce rana a na’urar ATM ɗin daga asusun mutum guda.
A jiya ne dai Bankin Zenith ya sanar wa masu ajiyarsa ta hanyar saƙon imel cewa, yanzu za su iya cire kuɗi daga asusunsu har Naira Naira 200,000 a kwacce rana daga na’urar ATM ɗin bankin a faxin ƙasar nan, ba tare da la’akari da bankin da aka yi katin ATM ɗin ba.
Amma sai dai bankin ya bayyana cewa, dokar kashiles wacce ta hana kowanne mutum cirar takardun Naira fiye da Naira 500,000 daga asusunsa a kowanne tana aiki har yanzu.
Akwai ƙishin-ƙishin ɗin cewa sauran bankuna ma za su shiga sahun Zenith ɗin wajen ɗabbaƙa wannna sabon canjin ƙa’ida duk da dai su ba su yaɗa nasu ƙudurin ba.
A baya dai bankuna da dama sun sanya takunkumin a kan cire Naira 20,000 a kullum daga na’urar ATM ɗinsu musamman ma ga katinan ATM ɗin da ba na bankunansu ba ne.
Wannan doka ta fara aiki ne tun a lokacin da ake ƙoƙarin sauya fasalin takardun kuɗin Nijeriya.
A Disamban shekarar bara ta 2022 ne dai Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙayyade adadin kuɗin da za a iya cira a asusu a kullum zuwa Naira 100,000 ga ɗaiɗaikun mutane, sai Naira 500,000 ga asusun kamfanoni.
Sannan cire kuɗi a na’urar POS da ATM zuwa Naira 20,000 a kowacce rana. Wanda ya fara aiki ranar 9 ga Janairu, 2023.