Daga BELLO A. BABAJI
Bankuna a Birnin Tarayya Abuja sun ƙara adadin kuɗin da ake iya cirewa zuwa Naira 50,000.
Rahotonni sun bayyana cewa bankunan Zenith da GT sun ƙara adadin daga N5,000 a watan da ya gabata.
Bankin GT dake hanyar filin jiragen sama a birnin yana biyan kwastomomi N50,000 aciki yayin da yake biyan N20,000 a ATM.
Wani jami’i ya ce hakan ya samu ne sakamakon yalwar kuɗaɗe da bankin yake da shi.
A ƴan kwanakin nan ne masu POS suke cazar kwastomomi N800 a kowacce N20,000 yayin da suke karɓar N2,000 a N50,000.
A ranar Laraba ne babban bankin Nijeriya, CBN ya bai wa bankuna umarnin fitar da isassun kuɗaɗe ga kwastomomi tare da shan alwashin hukunta waɗanda suka ƙi kiyayewa.