Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bankuna a Babban Birnin Tarayya, sun ƙara yawan adadin kuɗaɗen da za a iya cire zuwa Naira 50,000 a kowace rana.
Wani bincike da wakilinmu ya gudanar a ranar Talata ya nuna cewa bankunan da suka haɗa da Guaranty Trust Bank da Zenith Bank sun ƙara adadin kuɗin cirewa daga N10,000 da aka ba abokan ciniki a watan jiya.
A reshen GTBank da ke kan titin filin jirgin, an ba abokan ciniki damar cirar Naira 50,000 da katin ATM amma iyaka Naira 20,000.
Wani jami’in da ya zanta da manema labarai ya ce a yanzu haka bankin ya mallaki wasu maƙudan kuɗaɗe da ya sa aka ƙara kuɗin.
“Yanzu muna da ƙarin kuɗi kuma shi ya sa muke ba da ƙarin kuɗi.”