Barazana ga zaɓen 2023

Duk da cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da hafsoshin tsaron ƙasar sun tabbatar da cewa za a gudanar da zaɓen 2023 cikin lumana duk da matsalar tsaro da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar.

Sai dai kuma rahotanni sun nuna cewa ’yan Nijeriya na cikin fargaba game da yawaitar taɓarɓarewar tsaro a ƙasar. Hakazalika ana fargabar gudanar da zaɓen a wasu sassan ƙasar da har yanzu ba a daƙile matsalar ba.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta kuma tabbatar da taɓarɓarewar yanayin tsaro a cikin sanarwar da ta fitar a baya-bayan nan cewa rumfunan zaɓe 242 da masu rajista 142,261 suka yi rajista a ƙananan hukumomi 10 na Jihar Katsina na cikin babbar barazana ta tsaro kuma mai yiwuwa lamarin ya shafi babban zaɓe mai zuwa.

A wani labarin kuma, rahotannin da aka alaƙanta ga ƙungiyoyin fararen hula da abin ya shafa a ƙarƙashin kwamitin tuntuva tsakanin hukumomin tsaro kan harkokin zaɓe (ICCES), na nuni da cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC za ta iya fuskantar matsin lamba wajen gudanar da zaɓen 2023 a sama da yankuna 686 saboda ayyukan ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba a faɗin tarayyar Nijeriya.

Binciken da ƙungiyar ta gudanar ya nuna cewa yankunan da abin ya shafa sun kai ƙananan hukumomi 90 da kuma jihohi 18 na ƙasar. Daga cikin yankuna 686 da abin ya shafa, an gano 618 a arewa kaɗai, yayin da Kudu ke da 68.

An gano qasa da yankuna 336 da abin ya shafa a yankin Arewa maso Yamma inda 200 ke a Jihar Zamfara kaɗai. A Arewa maso Gabas, an gano akwai 168, inda Jihar Borno ke da unguwanni kusan 79 da ba za a iya gudanar da zaɓe ba. Kimanin unguwanni 114 da akasari ke cikin jihohin Kwara, Nasarawa, Neja da Filato ne lamarin ya shafa a shiyyar Arewa ta Tsakiya.

Hakazalika, an gano yankuna 55 a matsayin wuraren da ake fama da rikici a jihohin Abia, Anambra da Imo. A yankin Kudu maso Yamma, binciken ya nuna cewa an gano aƙalla yankuna 10 a jihar Ondo, musamman a ƙananan hukumomin Owo da Ose da kewaye.

A yayin da ake fama da matsalar rashin tsaro a wasu sassan ƙasar, ba za a iya tabbatar da tsaron jami’an INEC ba.

Babu shakka gwamnatin ta yi ƙoƙari sosai wajen kawar da fargaba da kuma tabbatar wa masu kaɗa ƙuri’a kariya a lokacin zaɓen 2023. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kuma umurci sojojin ƙasar da su daƙile ƙalubalen tsaro a ƙasar nan da watan Disambar wannan shekara. A cewar ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, Buhari ya umarci jami’an tsaro da su murƙushe ’yan bindiga da ’yan ta’adda.

Har ila yau, Ministan Yaɗa Labarai, Lai Mohammed, ya kuma tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa zaɓen 2023 ba ya fuskantar barazana ko kaɗan, ya ƙara da cewa, halin da ake ciki na rashin tsaro da ake fargabar shi ne babbar barazana ga gudanar da zaɓen 2023, jami’an tsaro za su daƙile.

Duk da haka, ba a daidaita ba da tabbacin da ayyuka masu dacewa ba. A maimakon haka, barazanar ’yan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya a Arewa maso Gabas, ’yan bindiga a Arewa maso Yamma, rikicin manoma da makiyaya a yankin Arewa ta Tsakiya, tayar da jijiyar wuya a yankin Kudu maso Gabas da miyagun ayyuka a Kudu maso Yamma da Kudu ta Kudu suna ƙaruwa. A wasu ƙananan hukumomin Katsina, Kaduna, Neja, Sokoto, Kebbi da Zamfara, yanzu kusan ’yan bindigar sun mamaye.

A ranar 25 ga Yuni, 2022, wata ƙungiya mai tsattsauran ra’ayi a majalisar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna ta fitar da wani faifan sauti na nuna adawa da duk wani nau’in yaƙin neman zaɓe a yankin. Sanarwar ta bayyana musamman ƙauyuka kamar Damari, Saulawa, Dogondawa a matsayin yankunan “babu yaƙin neman zaɓe”. Ana cigaba da samun irin wannan barazanar a wasu yankuna a yankin Kudu maso Gabas.

Sanarwar yiwuwar kai harin ta’addanci da ƙasashen Amurka da Birtaniya da Canada da Australia da sauran ƙasashen yammacin duniya suka yi wa ’yan ƙasar kan Abuja da wasu jihohin ƙasar ya ƙara fargabar zaɓen. Al’adar tashe-tashen hankula a sassan yankuna ƙasar ya ƙara dagulewa.

Hare-haren da aka kaiwa ofisoshin INEC a jihohin Ogun da Ondo alamu ne da ke nuna cewa tashin hankali zai biyo bayan zaɓen. Irin wannan munanan hare-hare sun faru a Imo, Enugu, Anambra da sauran sassan ƙasar. A Imo, an kai wa jami’an rajistar INEC hari a majalisar Ihitte-Uboma ta jihar.

Wannan shine lokacin da ya kamata a magance matsalar tsaro da ke barazana ga zaɓen. Mai yiyuwa ne idan har ba a shawo kan lamarin yadda ya kamata ba kafin zaɓen, wasu hargitsi na iya karuwa.

Rashin tsaro dai babbar barazana ce ga zaven 2023. A kare ofisoshin INEC da jami’ansu. Duk wani abu da zai kawo barazana ga zacen dole ne a magance shi a yanzu.

Ya kamata gwamnati ta tabbatar da cewa an samar da isasshen tsaro kafin zaɓe da lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓe. ’Yan sandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro dole ne su samar da isassun matakan tsaro don tabbatar da tsaron ƙasar.