Barazanar hari: DSS ta buƙaci a kwantar da hankali

Daga BASHIR ISAH

Biyo bayan sanarwar barazanar harin da Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja ya fitar, hukumar tsaro ta DSS ta bukaci jama’a kowa ya kwantar da hankalinsa.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun DSS ya fitar a ranar Lahadi, Dr. Peter Afunanya, ya ce an tuntube su daga sassa da dama dangane da sanarwar barazanar tsaron da Ofishin Jakadancin Amurka ya fitar.

A ranar Lahdi Ofishin Jakadancin Amurka da takwaransa na Birtaniya da ke Abuja, suka fitar da sanarwar falkarwa kan yiwuwar kai hare-hare a Abuja, babban birnin ƙasar.

Lamarin da ya sanya ofisoshin biyu suka yanke shawarar taƙaice harkokinsu a Abuja har sai abin da hali ya yi.

Mabambantan sanarwar da suka fitar sun nuna wuraren da ake shirin kai wa harin sun haɗa da makarantu da kasuwanni da wuraren ibada da gine-ginen gwamnati.

Sauran sun haɗa da otel-otel da manyan shaguna da wuraren taro da gareji motoci da dakunan cin abinci da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *