Barazanar matsalar tsaro ga zaɓen 2023

Assalam alaikum. Kamar yadda Ƙungiyar da ke hanƙoron tabbatar da ’yancin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce rashin hukunta waɗanda aka kama da laifi a zaɓukan ƙasar na baya da kuma gazawar gwamnati na magance matsalar tsaro na barazana ga aiwatar da babban zaɓen ƙasar na 2023.

A ranar 25 ga watan Fabrairu ne al’ummar Nijeriya za su zaɓi sabon shugaban ƙasa domin maye gurbin shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda ke kammala wa’adin shugabancinsa, tare da na ‘yan majalisar dokokin tarayya, bayan mako biyu kuma za su fita domin kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi.

An dai yi ta samun barazanar tsaro game da zaɓen daga ƙungiyoyi daban-daban a faɗin ƙasar, ciki har da ƙungiyoyin ‘yan bindiga a yankin Arewa maso yamma da kudu maso gabashin ƙasar, waɗanda ke yunƙurin daƙile yiyuwar zaɓen.

Wani bayani da ƙungiyar ta Human Rights Watch ta fitar a ranar Litinin ɗin nan ya nuna cewa har yanzu ƙasar ba ta ɗauki isassun matakan da za su kwantar da hankulan mutane ba kan cewa zaɓen zai tafi cikin lumana.

A cewar arahoton, tarihin zaɓukan Nijeriya ya nuna yadda zaɓukan ke cike da rigingimu da sauran laifukan zaɓe.

Ƙungiyar ta Human Rights Watch ta ce zaɓen Nijeriya na 2015 wanda ya bai wa shugaba mai ci Muhammadu Buhari nasara a matsayin ɗan takarar jam’iyyar adawa na farko da ya yi nasara zaɓen ƙasar shi ne ake gani wanda aka yi cikin kwanciyar hankali.

To amma an samu ‘yar hatsaniya a zaɓen 2019, ciki har da amfani da jami’an tsaro wajen yin barazana ga masu kaɗa ƙuri’a da kuma ‘yan dabar siyasa da ke yi wa ‘yan siyasa aiki.

Rahoton na Humar Rights Watch ya ce a ƙarƙashin dokokin kare haƙƙin bil’adama, wajibi ne gwamnati a matakin tarayya da kuma matakai na ƙasa su ɗauki duk matakan da suka dace wajen ganin jami’an zaɓe da ’yan jarida da kuma jami’an ƙungiyoyin masu zaman kansu ba su fuskanci kowane irin barazana ba a lokacin zaɓe.

Sai dai rahoton ya ce, duk da kiraye-kirayen da ake yi kan hukumomin Nijeriya su tabbatar da adalci a kan waɗanda aka kama da laifin hannu a rikice-rikicen zaɓe na baya, ƙungiyar ta Human Rights Watch ta gano cewa babu wani ci gaba da aka samu.

Ya ƙara da cewa, kwamitin da rundunar sojin Nijeriya ta kafa domin yin binciken zarge-zargen cin zarafi da kisan jami’ai masu alaƙa da zaɓe, an ba shi mako biyu ne kawai ya gabatar da bayanan da ya samu a watan Maris na 2019, sai dai shekara huɗu bayan haka, babu wani bayani daga gwamnati kan abubuwan da kwamitin ya gano.

A watan Janairu Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Nijeriya INEC, ta bayyana cewa za ta gudanar da zaɓukan ƙasar na 2023 a faɗin ƙasar, har da wuraren da ake fama da rikici, duk da matsalolin tsaro da ake fuskanta.

A jihjohin Arewa maso yamma, kamar Zamfara, da Katsina, ’yan bindiga na cin karensu babu babbaka tun bayan da matsalar ’yan fashin daji ta ƙazanta.

A Kudu maso gabashin ƙasar kuwa, kamar a jihar Imo, ana ci gaba da fuskantar barazanar ’yan bindiga da kuma mayaƙan IPOB, waɗanda ake zargi da kai hare-hare a kan ofisoshin hukumar zaɓen ƙasar da kuma cibiyoyin jami’an tsaro.

Daga MUSTAPHA MUSA, 07066778190.