Barcelona ce kan gaba a yawan cin ƙwallaye tsakanin manyan gasar Turai biyar kawo yanzu, wato La Liga da Premier League da Serie A da Bundesliga da Ligue 1.
Ranar Lahadi Barcelona ta doke Espanyol 3-1 a wasan mako na 12 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta kakar nan.
Kenan Barcelona ta zura ƙwallo 40 a wasa 12 a La Liga, karon farko da ta yi wannan ƙwazon tun bayan 1950/51 da ta ci 42 a irin wannan matakin.
Wadda ke biye da Barcelona a wannan bajintar a kakar nan ita ce Bayern Munich, mai 32 a raga a Bundesliga da kuma Paris St Germain mai 29, bayan karawa 10 a Ligue 1.
Bayan cin ƙwallaye da Barcelona ke yi, sannan tana tsare bayanta, wadda 11 aka zura mata a raga, kenan tana da rarar 29, bayan karawa 12 a La Liga.
Atletico Madrid ce kan gaba a Sifaniya, wadda ba a zura mata ƙwallaye da yawa ba a bana, bayan wasan mako na 12 a La Liga.
Atletico ta ci 18, yayin da bakwai suka shiga ragarta, kenan tana da rarar 11.
Barcelona tana matakin farko a kan teburin La Liga da maki 33 da tazarar maki tara tsakani da Real Madrid, wadda ta yi karawa 11.
Ranar Laraba Barcelona za ta je gidan Red Stars a Champions League daga nan ta ziyarci Real Sociedad a La Liga ranar Lahadi