Barcelona da Chelsea na rububin ƙulla yarjejeniya da Neymar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Makomar Neymar idan har ya rabu da PSG na cigaba da kasancewa cikin rashin tabbas a daidai lokacin da ɗan wasan tare da ƙungiyar ta sa suka amince da Shirin rabuwar nan ba da jimawa ba.

Sai dai mai yiwuwa burin ƙungiyoyin Barcelona da Chelsea waɗanda ke son ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan ya gaza cika, saboda ƙalubalen da kowannensu ke fuskanta.

A ɓangaren Chelsea, a yayin da ta kasance ƙungiyar da za fi dacewa da samun sauƙin sayen Neymar, ba lallai bane ɗan wasan ya amince da tayin komawa gare ta, la’akari da cewar ba samu tikitin buga gasar Zakarun Turai ta bana ba.

Ita kuwa Barcelona da za a ɓarje gumi da ita a gasar Zakarun Turan, ba ta da kuɗin ƙulla yarjejeniya da ɗan wasan, sai dai fa idan har ya amince ya sauya sheqa zuwa ƙungiyar Al Hilal da ke gasar ƙhwallon ƙafar Saudiyya, wadda majiyoyi ta ce a shirye ta ke ta miqa wa Barcelona shi a matsayin aro, tsawon kakar wasa guda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *