Barcelona na yunƙurin lashe La Liga na bana

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ranar Lahadi Espanyol za ta karɓi baƙuncin Barcelona a wasan mako na 34 a La Liga.

Ƙungiyoyin biyu sun tashi 1-1 ranar 31 ga watan Disamba a Camp Nou a karawar farko a kakar bana ta La Liga.

Kasancewar wasan na dabi ne, wataƙila a ranar Barcelona za ta lashe babban kofin ƙwallo na Sifaniya.

Rabon da Barcelona ta lashe La Liga tun kakar 2018/19, mai kofin 26 jimilla, amma Real Madrid ce mai riƙe da na bara.

Kawo yanzu idan aka buga wasannin mako na 34 a ƙarshen mako, zai rage saura fafatawa huɗu a ƙarƙare kakar bana, wato make 12 ne a kasa daga ranar ta Lahadi zai rage.

Barcelona tana mataki na ɗaya a kan teburi da maki 82 da tazarar maki 13 tsakani da Atletico Madrid ta biyu mai maki 69.

Real Madrid ce ta uku da maki 68, sai Real Sociedad mai maki 61 ta huɗu a kan teburi.

Barcelona za ta iya lashe kofin tun kan ranar Lahadi, idan Atletico Madrid ta kasa cin Villareal ranar Asabar 13 ga watan Mayu.

Haka kuma Barcelona za ta iya ɗaukar La Ligar tun kan ranar Lahadi, idan har Real Madrid ba ta iya doke Getafe ba ranar Asabar.

Haka kuma koda Barcelona za ta kasa cin wasan da suka rage mata, ya zama wajibi Atletico da Real Madrid su lashe sauran wasannin La Liga da ke gabansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *