Barka da Sallah: Matawalle ya jaddada alƙawarin magance matsalar tsaro a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar jihar sakamakon ayyukan ‘yan fashin daji don maido da zaman lafiya a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ran jajibirin Babbar Sallah a wata sanarwa da ya gabatar ga al’ummar jihar kan bikin Idul Kabir na bana.

A cewarsa, ƙalubalen rashin tsaron gwamnatinsa ta gaje shi ne daga tsohuwar gwamnati da ya gada shekaru biyu da suka gabata, yana mai jaddada cewa shirin sasanci, zaman lafiya da tattaunawa game da batun sulhu a tsakanin masu tayar da ƙayar baya wanda gwamnatinsa ta ƙirƙiro ya haifar da kyakkyawan sakamako wanda ya haifar da kwanciyar hankali a jihar bakin gwargwado.

Gwamnan wanda ya yaba da ƙoƙarin hukumomin tsaro da ke aiki a jihar, ya yaba tare da yaba wa goyon baya, addu’o’i da haɗin kai da ‘yan ƙasa ke bai wa gwamnatinsa musamman ta hanyar addu’o’i kuma ya buƙace su da su ci gaba da hakan a koyaushe.

Matawalle ya yi nuni da cewa gwamnatinsa na nan na ƙoƙari wajen cika alƙawuran yaƙin neman zaɓenta duk da ƙarancin tattalin arziki da kuma barazanar rashin tsaro wajen ganin an samar da hanyar samar da ribar dimokuraɗiyya ga ɗaukacin al’ummar Jihar.

Gwamnan wanda ya yaba bisa irin fahimtar da ma’aikatan gwamnati suka yi ga gwamnati, ya ce gwamnatin sa ta amince da a fara biyan albashin watan Yuli a tsakiyar wata don su yi bikin Sallah ba tare da wata matsala ba.

Yayin da yake yi wa al’ummar musulmin jihar murnar zagayowar bikin Sallah, gwamnan ya buƙace su da su tuna da irin kyawawan halayen da aka wajabta musu a kan Idul Kabir sannan su ci gaba da kasancewa masu kula da ‘yan’uwansu.