Bashin da ake jibga wa Nijeriya ke jawo gwamnati neman sayar da kadarorinta – Ɗanpass

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana cewa yawan basukan da gwamnatin Nijeriya ke yawan karɓowa daga ƙasashen waje na neman tilasta ƙasar cefar da wasu muhimman kadarorinta.

Ɗan Saran Kano, Alhaji Gambo Ɗanpass shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano cikin makon nan.

Ana raɗe-raɗin Gwamnatin Nijeriya da yiwuwar za ta cefanar da asibitocin Gwamnatin Tarayya ga ‘yan kasuwa da sauran ma wasu kadarorin, wanda Ɗanpass ya bayyana hakan a matsayin illolin bashin da ƙasar ke karɓowa.

Ya ce dama illar cin bashi kenan da zai kasance ƙasa za ta zama ba ta da ‘yanci da madafa za ta koma kame-kame yadda hakan zai jefa al’ummar ƙasa wani hali don haka Gwamnatin Tarayya ya kamata ta yi hattara.

Ɗan Saran na Kano ya ce da za ta yi kyakkyawan duba saita tura wakilai ƙasar Zimbaguwae taga me yake faruwa a sakamakon yawan cin bashi.

Ya ce wannan shiri na cefanar da asibitocin gwamnati in aka yi zai daɗa jefa mutane ne a cikin wahala.Dama tsari ne na wasu mutane na jari hujja da za a danne talakawa don ya zama wajibi al’ummar Arewa su yi hattara su zama tsintsiya ɗaya maɗauri ɗaya don kauda irin wannan cin kashin kaji da siyasa take kawota.

Ya ce ya kamata ‘yan Arewa su yi karatun ta natsu su san wane fasali ya kamata su yi a haɗa ƙarfi da ƙarfe a tabbatar da zaɓen da za a yi, wa za a zaɓa, amma matuƙar ba a natsu ba, aka faɗa tarkon ɓera to za a zama babu madogara da tasiri a Arewa.

Alhaji Gambo Abdullahi Ɗanpass ya ce ya zama wajibi mu guji siyasar gaba a haɗa ƙarfi da ƙarfe a yi magana da murya ɗaya a Arewa kamar yadda wasu sassan ƙasar nan suke; amma nan yankin Arewa ba shugabanni masu faɗa a ji da za su ce a yi abinda ya kamata.

“Ya kamata malamai na addini su yi amfani da tasirinsu su riqa faɗakar da mutane cewa ana neman mafita a halin da Arewa ta tsinci kai a ciki,” inji Ɗanpass.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *