Basussuka: Bankin Duniya ya nema wa ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi rangwame

Daga AMINA YUSUF ALI

A ranar litinin ɗin da ta gabata ne Shugaban bankin Duniya, David Malpass ya nemi arzikin ƙasashen da suke bin bashi da su ƙara ɗaga ƙafa ga ƙasashen da suke bin bashi. 

Malpass ya bayyana cewa, abinda ya tilasta shi yin wannan kira mai kama da neman arziki shi ne, ganin yadda tattalin arzikin ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi ya jijjiga a sakamakon annobar cutar Kwarona wacce ta jigata ƙasashen Duniya a shekarar 2020.

A cewarsa, cin basussukan shi kaɗai ne abinda zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin ƙasashen tare da taimaka musu wajen yaƙi fatara da talauci.

Ya ƙara da cewa, yanzu haka wa’adin biyan bashin ƙasashe da  dama zai ƙare a ƙarshen wannan shekarar a cewar sa. Abinda ya ce ana buƙatar samar da maslaha a kan batun. Wato a cewar sa, za a jingine basussukan tare da ƙarin lamuni ga ƙasashen. Domin su kansu suna cikin halin fafutukar yadda za su farfaɗo daga dukan da annobar COVID-19 ta yi ga tattalin arzikinsu.

Bincike ya nuna cewa, a yanzu haka dai basussukan da ake bin waɗancan ƙasahe marasa ƙarfi ya tasam ma, Dalar Amurka, $860  wato billiyan ɗari takwas da sittin. Alƙalumman da ba a taɓa kai wa ba, a tarihi.