Batun barazanar yi wa Buhari juyin mulki shaci-faɗi ne – Hedikwatar tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Asabar ne daraktan yaɗa labarai na hukumar rundunar sojin Nijeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya fito ya nesanta abinda wata kafar yaɗa labarai ta intanet ta alaƙanta da cewar “Hukumar tsaro ta gargarɗi sojoji akan su fita shirgin mulkin Buhari da kuma yunƙurin yi masa juyin mulki.”

Kakakin rundunar, Birgediya-Janar Nwachukwu ya ce rahoton ƙarya ne kuma aiki ne na masu tada fitina a ƙasar.

Wani ɓangare na sanarwar yana cewa, “An jawo hankalin hedikwatar tsaro a kan wata ƙarya da wata jarida ta yanar gizo ta Naija News House ta buga kan sojojin Nijeriya da ke gargaɗin ‘yan siyasa da jami’ai kan juyin mulkin da ta ta’allaƙa da Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar soji.

“Rubutun aiki ne na wasu maɓarnata kuma maƙiya ci gaban ƙasa. Ƙoƙari ne da gangan da ƙididdiga don yaudarar jama’a da nufin haifar da rashin jituwa a cikin harkokin siyasa.”

Hakazalika, jami’in ya bayyana cewa, rundunar soja ba ta da alaƙa da siyasa ko hannu a wani ɓangaren siyasa, don haka ‘yan Nijeriya su guji rahoton gidan jaridar.

Nwachukwu ya ce manyan jami’an su da sauran sojojin Nijeriya ba sa buƙatar “gargaɗi akan hamɓarar da gwamnatin Shugaba Buhar,” ya ce jami’an su masu biyayya ne da girmama kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma Shugaban Askarawan ƙasar, wanda iya haka kawai za a gane cewa labari ne kawai na ƙanzon kurege.

“Hukumar Sojin Nijeriya hukuma ce mai kima da ita ma take tare da farar hula, kuma wadda ta tsayu wajen kare al’umma da kuma dorewar dimukraɗiyya a ƙasar.

“Hukumar kuma za ta ci gaba da tsayuwa wajen kare kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma nuna soyayya ga mulkin dimukaraɗiyya ta hanyar taimaka wa fararen hula a kowane lokaci,” inji shi.

Haka kuma, sanarwar ta ce rundunar sojin ta Najeriya ta ta yi mai yiwuwa ta kowane hali a yunƙurin jawo sunanta cikin harkokin siyasar cikin gida.