Akwai wani al’amari mai matuƙar tayar da hankali da ban tausayi kan yadda ake amfani da yara masu ƙananan shekaru maza da mata don yin aiki ko bauta a gidaje da sauran wurare da suka haɗa da shaguna, otel-otel, wuraren kwana na manyan makarantu ko ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’o’i.
Akasarin yaran ’yan ƙasa da shekaru 15 ne kuma ana ɗaukarsu ne da nufin yin aikace-aikacen da suka haɗa da shara, wanke-wanke, wanki, goge-goge, ɗebo ruwa da rainon jarirai da kula da yayayyun yara da makamantansu.
Mafi yawan yaran ana kawo su cikin birni daga ƙauyuka lokaci zuwa lokaci, ta hanyar uwar aikatau bisa amincewar da yawa daga cikin iyayensu don tunanin samar musu da abin duniya da bai taka kara ya karya ba, musamman idan aka yi la’akari da irin illar da aikatau ke haifarwa a cikin al’umma.
Idan aka yi duba izuwa aikatau za a tabbatar da illolinsa masu yawa waɗanda su ke shafar yaran da ke yinsa da kuma yaran da iyayensu ke ɗaukar ’yan aikin kai har ma da sauran al’umma baki ɗaya. Babbar matsalar ita ce yadda ake tauye wa ’yan aiki haƙƙinsu da ya kamata su samu a lokacin ƙuruciyarsu.
Misali, ilimi na daga cikin haƙƙin da ya zama tilas a bai wa yara don inganta rayuwarsu da nufin samar da jagorori na gari a nan gaba, sai dai wannan damar takan kuɓuce wa akasarin ‘yan aiki, musamman yadda ake amfani da su wajen bautar da su a lokutan da ya kamata a ce suna halartar makarantu don inganta rayuwarsu.
Akwai tabbacin irin yadda ake maida su tamkar bayi a wasu wurare, wanda ko kare ba a yi masa haka, inda za a ga ana yi musu tsawa ana hantararsu kai wasu har dukansu ake yi, a kuma hana su abinci, musamman in sun saba umarnin da uwar ɗakinsu ta ba su.
Hakazalika, idan aka ga makwancinsu a wasu gidajen ko kajin gidan gona sun fisu wajen kwanciya mai kyau, ga rashin hutu da kuma rashin samun wadataccen barci wanda hakan ka iya yin barazana ga lafiyar jikinsu, kuma duk da waɗannan ƙuncin, ana biyansu wani ɗan abu da bai taka kara ya karya ba, wanda a wasu lokutan kuma, uwayen aikatau ɗin ne ke kwashe kuɗi su bai wa iyayen yaran sauran canjin.
Wata babbar matsalar aikatau ita ce yadda jahilci ke addabarsu a inda yawancinsu ba su san yadda za su bauta wa Ubangijinsu ba, sai ka ga tsarki da cikakkiyar alwala na gagararsu kuma iyayen ɗakinsu ba su cika damuwa da su riƙa koyar da su abubuwa masu amfani, musamman yadda za su riqa gabatar da ibada tunda ta zama tilas a rayuwarsu, wannan yakan jawo musu ballagazanci da rashin kamun kai idan girma ya zo musu wanda ka iya jansu ga harkar banza, ko kuma yawon ta zubar don da yawansu ba su iya komawa karkararsu inda suka fito, mazan kuma su zamto marasa aikin yi wanda illarsa ta ke da yawa a cikin al’umma.
Kodayake ba dukka aka taru aka zama ɗaya ba, don kaɗan daga cikin iyayen ɗakinsu sukan turasu makarantun Islamiyya na Yamma ko na dare, amma akasari wannan bai cika samuwa ba. Haka kuma tsangwama da barazanar hukuncin muzantawa ko kuma kora gaba ɗaya na zama fargaba a zukatansu.
Kamar yadda muka faɗa a baya, illar aikatau ta kan shafi masu ɗauko su, don wasunsu sukan fita aiki ko makaranta tun safe sai yamma ko dare su bar ’yar aiki da kula da yara ƙanana, wanda ita kanta ba ta da cikakkiyar tarbiyar da za ta kula da kanta ballantana har ta koya wa yaran, a irin haka ne yaran kan tashi da dukkan abin da suka ga tana yi ko da kuwa marasa kyau ne.
Wata matsalar kuma ita ce yadda wasu masu gida ko yara matasa da ke gidan kan lalata ’tan aiki bisa tursasasu su amince da buƙatarsu.
A haƙiƙanin gaskiya wannan matsalar tana buƙatar haɗa hannuwa domin magance ta musamman yadda ta ke barazanar lalata tarbiyar yara a matsayinsu na manyan gobe.
Da farko iyayen yaran na da muhimmiyar rawa wajen rage wannan matsalar, Kodayake halin ƙunci na talauci na daga cikin babban dalilin da ke jawo matsalar, amma duk da haka bai dace su riqa bada ’ya’yansu don kaiwa birni bisa rashin sanin takamaiman gidan da za a kai su da kuma halin da su ke ciki a can ba.
Kuma duk akan ɗan abin da bai kai ya kawo ba. Duk da a rayuwar duniya Allah da ya halicci bayinSa ya sanya wasu sun fi wasu, kuma wasu sai sun yi wa wasu aiki za su samu abin da za su ci, to in har ya zama dole a yi aikatau, to iyayen yaran su sanya sharaɗi akan duk mai buƙatar ’yarsu don yin aikatau, to dole su sanyata a makaranta don samun ilimi musamman don sanin yadda za su gabatar da addininsu.
Jaridar Blueprint Manhaja na kira ga gwamnatoci da hukumomin da ke da alhakin kare mutuncin yara su yunƙuro don sanya kwakkwarar doka akan yadda ake azabtar da yara da sunan aikatau, a kuma saka doka mai tsauri ga duk wanda aka same shi da cin zarafi ko kuma bautar da yara.
Haka kuma, ya kamata gwamnatoci su riqa kafa wuraren koyar da sana’o’i don yara maza da mata, musamman a yankunan karkara da suka haɗa da ɗinki, saƙa, rini, ƙere-ƙere da girke-girke da aikin kafinta da dai sauransu da nufin samar musu da madogara a gaba. Wannan zai hana su yawan fitowa neman abin duniya ta hanyar da ba ta dace ba.
A ƙarshe, jama’a su bada gudummawa don hana gurɓata tarbiyyar yara. Masu musguna wa ’yan aikinsu, su ma su ji tsoron Allah, su sani rayuwa ba ta da tabbas, don kuwa su ma yaransu ka iya kasancewa a irin wannan halin, kuma su lura da cewar komai karen daɗewa, duk abin da ka shuka shi za ka girba.