Batun dokar hana hadahada da kuɗin kirifto

Kwanan nan ne Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya kaɗa hantar wasu ‘yan Nijeriya lokacin da ya tunatar da bankuna da sauran hukumomin da ke kula da hadahadar kuɗi cewa dokar nan da ta haramta amfani da kuɗin intanet, wato kuɗin kirifto (cryto currency), ta na nan daram. Karo na uku kenan a cikin shekara biyar da babban bankin ya yi magana kan harka da irin wannan kuɗi da ake ganin ta na tattare da babban ganganci a cikin ta.

Sakamakon hakan, bankuna sun shiga soke duk wani asusu da aka buɗe da sunan yin harka da irin wannan kuɗin. Majalisar Dattawa kuma ta gayyato Gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele, domin ya yi mata bayani kan matsaloli da kuma alfanun da ke cikin hulɗa da wannan kuɗi na kirifto, saboda akwai masu cewa kuɗi ne na zahiri waɗanda za su taimaka wajen haɓaka tattalin arzikin Nijeriya. Abin da ya haifar da ƙara tado maganar a yanzu shi ne akwai masu cewa yawancin hadahadar kuɗin kirifto ana yin ta ne ta hanyar da ba za a iya bin bahasin kuɗin ba, kuma ba sai mutum ya san da wa ya ke yin mu’amala ba, wanda hakan ya haifar da tsoron cewa masu aikata laifi za su iya amfani da kuɗin ta hanyoyin da ba su dace ba, misali su juya kuɗin sata ko na muggan ƙwayoyi ko ma su ɗauki nauyin aikata ta’addanci.

A cikin Maris 2018, babban bankin ya gargaɗi ‘yan Nijeriya da su yi kaffa-kaffa da zuba jari cikin harkar kuɗin kirifto don kauce wa faruwar irin badaƙalar nan ta ‘Mavrodi Mundial Moneybox’ (MMM) da aka taɓa yi a shekarar 2017 wadda ta jawo wa miliyoyin ‘yan Nijeriya asara da karayar arziki, yayin da ‘yan kasuwa da dama su ka rasa jarin su ta hanyar damfara. Hukumar Inshorar Zuba Jari ta Nijeriya (NDIC) ta faɗa cewa aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 3 ne su ka yi asarar naira biliyan 18 a waccan badaƙalar ta MMM a tsakanin 2016 da 2017.

Babban Bankin Nijeriya ya nanata cewa dillalai da masu zuba jari cikin harkar kowane irin kuɗin kirifto a Nijeriya ba su da kariya a dokar ƙasa. Ya ƙara da cewa kuɗaɗen kirifto irin su ‘bitcoin’, ‘ripples’, ‘monero’, ‘litecoin’, ‘dogecoin’ da ‘onecoin’ da kuma hanyoyin canjin kuɗi irin na ‘NairaEx’ ba su da lasisi kuma ba su cikin tsarin CBN, saboda haka ba kuɗin gaske ba ne a dokar Nijeriya. Don haka babban bankin ya gargaɗi ‘yan Nijeriya a kan kada su zuba jari a kuɗin kirifto saboda duk wanda ya yi hakan, to duk abin da ya faru shi ne ya janyo wa kan sa.

Shi dai kuɗin kirifto, wata irin dukiya ce a yanar gizo da aka ƙirƙira a matsayin hanyar yin musanya inda ake amfani da abin da ake kira ‘cryptography’ (wata fasahar rubutu da warware bayanan sirri) don a samu gudanar da hadahada, mallake hanyar ƙirƙiro wasu sabbin kuɗin, sannan a tabbatar da tiransifa ɗin dukiya.

Tun a cikin Janairu 2017, bankin CBN ya fitar da sanarwa ga bankuna da sauran hukumomin hadahadar kuɗi a kan batun harka da kuɗin yanar gizo a Nijeriya. Bankin ya yi gargaɗin cewa ya gano ana amfani da kuɗin yanar gizo a kasuwannin hadahadar kuɗi a wurare daban-daban a duniya waɗanda ba su cikin tsarin doka.

Haka ita ma Hukumar Kula da Musayar Kuɗi ‘(Securities and Exchange Commission’, SEC) ta gargaɗi ‘yan Nijeriya a kan kada su kuskura su zuba jari a kuɗaɗen yanar gizo irin su ‘Bitcoin’, ‘Swisscoin’ da ‘OneCoin’, ta na mai nuni da cewa babu mutum ɗaya ko kamfani ɗaya da ke gudanar da harkar wannan kuɗin da ita ko wata hukumar kula da hadahadar kuɗi a Nijeriya ta yarda da shi. Hukumar ta nanata cewa akwai ɗimbin haɗari da yiwuwar masu zuba jari su yi asarar kuɗin su ta wannan hanyar da waɗannan kamfanonin ke gudanarwa, ciki har da tsare-tsaren damfara na ninka kuɗi.

NDIC, tare da haɗin gwiwar CBN, sun kafa wani kwamiti da zai yi nazarin yadda harkar kuɗin nan na yanar gizo mai suna ‘Bitcoin’ ta ke ƙara bunƙasa. A cewar Manajan Daraktan NDIC, Alhaji Umaru Ibrahim, hukumar za ta dubi kyau da rashin kyan kuɗin da kuma tasirin sa ga tsare-tsaren kashe kuɗi a Nijeriya da ma yadda za a kare muradin kwastomomi. Ya ce: “Tsarin ninka kuɗi sabon al’amari ne na manajojin harkar kuɗi da su ka saɓa wa doka waɗanda ake kiran su da ‘wonderbanks’, waɗanda su ke ci gaba da damfarar jama’a kuɗin su da su ka sha wuya wajen samu. Wannan lamari ya na haifar da damuwa saboda duk da yawan gargaɗin da mu ke ta yi a cikin tsawon shekaru, jama’a su na ta aukawa cikin zambar da ake yi masu. Mu na so mu nanata cewa manajojin hadahadar kuɗi masu karya doka ne domin CBN bai ba su lasisin karɓar kuɗin jama’a ba, kuma masu ba su kuɗin ba su da kariyar tsarin inshora na NDIC”.

Ita ma Majalisar Dattawa ta shigo cikin maganar ne a daidai wannan lokaci kuma ta tattauna kan yadda ake yawaita amfani da kuɗin yanar gizo, ‘bitcoin’, da shirye-shiryen ninka wa mutane kuɗi a Nijeriya. A cikin wani ƙudiri mai suna, “Buƙatar gaggawa ta a binciki ƙara yaɗuwar ‘Bitcoin’, wanda wani samfur ɗin kuɗin kirifto ne, don tabbatar da alfanun sa wajen zuba jari a Nijeriya”, Majalisar Dattawan ta jaddada cewa ban da kasancewar ƙaruwar zuba jari a ‘bitcoin’ har ma ya zama ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da ake bi ana zuba jari a ƙasar nan, ana nuno yadda ake hadahada da shi a bayyane a faɗin ƙasar nan a gidajen talbijin da na rediyo na cikin gida, musamman ga ‘yan Nijeriya waɗanda ba su san abin da ka je ya dawo ba.

Abu muhimmi shi ne bayanai daga ‘Local Bitcoins’, wani kamfani da Bitcoin ya kafa, sun nuna cewa Nijeriya ce ta biyu a hadahadar Bitcoin a duniya a cikin 2017, har ta zarce manyan ƙasashen nahiyar Turai, Birtaniya da Amurka. Babu shakka za a iya danganta hakan ga ɗimbin fatara da yunwar da ke akwai a ƙasar da kuma burin yawancin ‘yan Nijeriya na kuɗancewa a dare ɗaya.
Saboda haka dai jaridar Manhaja ta na kira ga CBN, NDIC, SEC da Hukumar Wayar da kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) da su zage damtse wajen aikin su na tabbatar da bin doka da kuma wayar da kan jama’a don ‘yan Nijeriya su kauce wa faɗawa cikin tarkon ‘yan damfarar da za ta sanya su rasa kuɗin da su ka sha wahala su ka samu, wanda za su iya kauce wa faruwar hakan idan har su na da cikakkiyar masaniya daga gwamnati.