Daga BASHIR ISAH
Ƙungiyar Dillalan Fetur Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (IPMAN) da ta masu dakon mai, wato ADITOP a taƙaice, sun ƙaryata batun cewa akwai shirin cilla kuɗin fetur zuwa Naira 700 kan lita guda.
Sun ƙaryata batun ne a wata zantawa da aka yi da su ranar Asabar a Abuja.
Ƙungiyoyin sun ce babu ƙamshin gaskiya cikin rahotannin da aka yaɗa a kan batun ƙarin farashin man.
A cewarsu, yanayin kasuwa ke tilasta ƙarin kuɗin fetur, kuma duba da yanayin kasuwar canji a halin yanzu babu buƙatar ƙarin farashin man sai dai hasashe kawai.
Wasu ‘yan kasuwa sun yi hasashen cewar farashin fetur ka iya haura sama da N700 a yankin Arewa, sannan kimanin N600 a Legas da zarar suka fara shigo da man daga ƙetare daga watan Yuli.