Batun sace dalibai, a tuhumi Buhari – Ezekwesile

Da hadin bakin Buhari a sace daliban Kankara- Ezekwesile

Tsohuwar ministan ilmi a zamanin gwamnatin Obasanjo ta ce, tana ganin da hadin bakin Buhari a satar yaran da aka yi, dan haka bata ga dalilin da zai sa a jinjina masa ko gwamnatin sa ba.

Tsohuwar Ministan wacce ita ce, ta shirya zanga zangar sace yan makarantar Chibok, ta ce akwai bukatar a tuhumi shugaba Buhari ya yi bayani akan me ya faru? A cewar ta saboda abin ya faru ne, jim kadan bayan ziyarar hutun kwana 7 da shugaban ya kai jihar. Dan haka “kamata yayi shugaban a tuhume shi maimakon a yaba masa”

“Kila dai ina zaton shugaba Buhari ya tura yaran ne su je yawon bude idanu wurin yan ta’addar” a cewar tsohuwar ministan. ” A saboda haka ba zamu yadda shugaba Buhari ya raina mana wayo ba”

Ta kara da cewa “kasashe da dama a yau suna mana dariya, suna cewa “su wa wadannan mutanen za su raina wa hankali?”

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*