Bauchi: Za a kammala sansanin alhazai kafin Hajjin bana

Daga WAKILIN MU

Gwamnatin Jihar Bauchi ta bada tabbacin cewa, za ta kammala aikin gina katafaren sansanin alhazai na ƙasa-da-ƙasa da ta sa a gaba kafin aikin Hajjin 2021 ya kankama.

Sakataren Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai na jihar, Alhaji Abubakar Babangida Tafida (Tafidan Giade), shi ne ya bada wannan tabbaci yayin ziyayar da ya kai a sansanin a ranar Alhamis da ta gabata don gane wa idanunsa yadda aiki ke gudana.

Jim kaɗan bayan kammala ziyarar, Babangida Tafida ya shaida wa manema labarai cewa, aikin sansanin alhazan na ɗaya daga cikin ƙudurorin gwamnatin Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad na son ganin sansanin alhazai na Jihar Bauchi ya zama kan gaba bisa ga saura.

Sakataren ya nuna gamsuwarsa dangane da yanayin aikin da ya gani a sansanin. Tare da cewa, gwamnati ta zuba dukiya sosai wajen ƙoƙarin samar da sansanin domin kula da walwalar alhazan Bauchi.

Ta bakin Tafida, “Na gode wa Allah da Ya bai wa Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad hikimar assasa wannan ƙasaitaccen aiki wanda zai bai wa maniyyata da jami’ai damar walwala yadda ya kamata.”

Kazalika, Sakataren ya ce ziyarar tasa za ta taimaka wajen saka ƙaimi ga injiniyoyin da ke aikin sansanin.

Daga nan, jami’in ya leƙa masallacin Juma’a na sansanin inda ya yi Sujadar Godiya domin nuna godiyarsa ga Allah game da aikin sansanin.

Tun farko, sa’ilin da yake zagayawa da sakataren yana nuna masa matsayin aiki, injiniya mai kula da aikin Engr. Isa Babayo, ya ce an cim ma kashi 95 cikin 100 na aikin. Daga nan, Babayo ya bada tabbacin cewa akwai yiwuwar su kammala aikin a cikin lokacin da aka tsayar.

Duka waɗannan bayanai sun fito ne ta hannun jami’in labarai na Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai na Jihar Bauchi, Muhammad Sani Yunusa.