Bawa ya kama hanyar kafa tarihi a hukumar EFCC

Daga FATUHU MUSTAPHA

A halin da ake ciki, Abdulrasheed Bawa, ɗan shekara 40, ya kama hanyar kafa tarihi na zama mai mafi ƙarancin shekaru da zai shugabanci Hukumar Yaƙi da Zambar Kuɗaɗe da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa (EFCC).

A ranar Talata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunan matashin don neman amincewarta kan naɗa shi sabon shugaban EFCC.

Bayanai sun nuna Bawa ƙwararre ne a fannin bincike dangane da batutuwan da suka shafi maguɗin kuɗi da sauran laifuka da suka danganci tattalin arziki.

Tun bayan dakatar da shugaban riƙo na EFCC Ibrahim Magu, a ranar 6 ga Yulin 2020, hukumar ta ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin kulawar Ahmed Umar.

A wasiƙar da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Ibrahim Lawan, Buhari ya ce ya wannan ne daidai da dokar EFCC ta 2004

Yayin da wasu ‘yan ƙasa ke yabon Shugaba Buhari bisa zaɓo Bawa don shugabancin EFCC har ma da fatan Majalisar Dattawan ta hanzarta yin abin da ya kamata, shi kuwa Magu cewa ya yi sam babu adalci cikin al’amarin. Magu ya faɗi hakan ne ta bakin lauyansa Tosin Ojaomo.