Bayan faɗuwar APC zaɓe a Katsina, Masari ya sallami wasu jiga-jigai a gwamnatinsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya amince da dakatar da naɗin kwamishina da sakatarorin dindindin guda biyu da kuma shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jihar nan take.

A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin jihar, Muntari Lawal (SSG) ya fitar, ya ce jami’an da abin ya shafa sun haɗa da Alhaji Tasi’u Dahiru-Dandagoro, kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri.

Sauran sun haɗa da Sakatariyar na dindindin, Manufofin ci gaba mai ɗorewa, Hajiya Fatima Ahmed, Sakatariyar dindindin ta Ma’aikatar Noma da Albarkatun Ƙasa, Alhaji Aminu Waziri.

Hakazalika, Masari ya sake tabbatar wa Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Alhaji Yusuf Barmo naɗin nasa.

SSG ya ce dakatar da naɗin nasu wani ɓangare ne na yin wasu tsare-tsare da gyare-gyare a cikin gwamnati.

“Dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da na gwamnati da abin ya shafa an umurce su da su miƙa duk kadarorin gwamnati da ke hannunsu ga sakatarorin dindindin ko kuma manyan daraktoci kamar yadda lamarin ya kasance,” inji Lawal.