Bayan kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Tinubu…

*Atiku da Obi za su cigaba da yaƙin
*Tinubu ya yi maraba da hukuncin
*Buhari ya tsomo baki
*Tinubu ya nuna gwanintar mulki a kwana 100 – Ministan Labarai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta tabbatar da nasarar Zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban kotun, Mai shari’a Haruna Tsammani ya ce matakin hukumar Zaɓe na ayyana Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen 25 ga watan Fabrairu, ya dace.

Matakin na zuwa ne bayan kotun ta kori ƙarar ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam’iyyar adawar Nijeriya, Atiku Abubakar da maraicen Laraba.

Shi, da Peter Obi na jam’iyyar Labour da kuma jam’iyyar APM, sun nemi kotun ta soke nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaven Fabrairu.

Sai dai, ba a ga ‘yan adawa irinsu Atiku da Peter Obi a zaman kotun na ranar Laraba ba, yayin da manyan jami’an gwamnati ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje suka shafe tsawon wuni suna sauraron hukuncin kotun.

Da farko, kotun ta yi watsi da ƙarar Peter Obi na jam’iyyar LP da ta jam’iyyar APM.

Ta kuma ce duk ƙararrakin, waɗanda aka shigar don neman a soke cancantar zaɓen Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, ba su da tushe.

Alqalan kotun biyar wajen gabatar da hukuncin, wanda suka shafe tsawon wunin ranar Laraba, suna gabatarwa.

Sun riƙa karɓa-karɓa wajen yin bita da karanta hujjoji, tare da tsefe bayanai, kafin bayyana matsayarsu a kan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar.

Atiku da Obi za su cigaba da yaƙin:

‘Yan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyun Labour Party (LP), Peter Obi, da Jam’iyyar PDP, Abubakar Atiku, duk sun yi watsi da hukuncin Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa (PEPC) da ta tabbatar da za en Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Ku tuna kotun, a ranar Laraba, ta tabbatar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen Shugaban Ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu, 2023 a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Kotun ta bayyana cewa ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, bai samu nasarar tabbatar da kokensa na neman tsige Tinubu daga muƙaminsa ba.

Kotun ta kuma yi fatali da ƙarar da LP da Obi suka shigar kan rashin cancanta yayin da ta yanke hukunci kan ko Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta dawo da Tinubu kamar yadda aka zaɓe shi da rinjayen ƙuri’un da aka kaɗa.

Da yake magana ta bakin tawagar lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Dr Livy Uzoukwu (SAN) bayan zaman kotun a daren Laraba, Obi ya sha alwashin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun ta yanke.

Tsohon Gwamnan na Anambra ya yi gargaɗin cewa idan ba a kula ba, hukunce-hukuncen zaɓe za su ɓace a ƙasar, yana mai jaddada cewa ya kamata a riqa gudanar da shari’a a kotu.

Ya jaddada cewa masu shigar da ƙara da ba su gamsu da sakamakon zaɓe ba na iya neman taimakon kansu idan suka ci gaba da fuskantar wahalar kafa shari’arsu sakamakon cikas daga cibiyoyin gwamnati kamar INEC.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a lokacin da yake magana ta bakin tawagar lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Chris Uche (SAN) a daren Laraba, ya ce ya samu hukunci ne kawai daga kotu ba tare da yin adalci bisa tsarin doka ba.

Ɗan takarar na PDP ya ce yana sa ran samun sakamakon da zai ƙarfafa amfani da na’urorin zamani wajen inganta gudanar da zave, gaskiya da riƙon amana ta yadda ‘yan Nijeriya za su yi imani da dimokuraɗiyya.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba, kuma ya sha alwashin tunkarar Kotun Ƙoli domin ta yi watsi da zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.

Ya ce: “An yanke hukunci, amma ba mu samu adalci ba. Abin farin ciki, Kundin Tsarin Mulki ya ba mu damar ɗaukaka ƙara.

Tinubu ya yi maraba da hukuncin:

Tuni Fadar Shugaban Nijeriya ta fitar da sanarwa, inda ta ce Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin kotun cike da tsananin sanin nauyin da ke kansa, da kuma shirin hidimtawa dukkan al’ummar Nijeriya.

Shugaban na Nijeriya ya kuma bai wa al’ummar Nijeriya tabbacin mayar da hankali wajen cika ƙudurinsa na samar da ƙasa mai haɗin kai da zaman lafiya da bunƙasar arziƙi.

Tinubu ya kuma ce ya yaba wa tsayin daka da jajircewar bin diddigin komai da kuma ƙwarewa daga alƙalan kotun biyar a ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsammani ga fashin baƙin doka.

Tinubu ya ce ya yi imani cewa ‘yan takarar shugaban ƙasa da jam’iyyun siyasar da suka yi amfani da ‘yancin da doka ta ba su dama wajen shiga babban zaɓen da kuma bin tafarkin zuwa kotu, sun tabbatar da matsayin bin tafarkin dimokraɗiyyar Nijeriya.

Ya kuma buƙaci su zaburar da magoya bayansu wajen yin amanna da aƙidar kishin ƙasa, ta hanyar mara wa gwamnatinsa baya don bunƙasa rayuwar duk ‘yan Nijeriya.

Atiku bai gabatar da shaidun da suka dace ba – Kotu

Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen dai ta yi watsi da ƙorafin Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP da neman a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihohin Kano da Legas.

Ta ce masu ƙorafin ba su shigar da Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso ba a ƙararsu, duk da yake su ne suka ci mafi rinjayen ƙuri’un da aka kaɗa a jihohin biyu.

Haka kuma ta kori bahasin ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar wanda ya zargi Bola Tinubu da mallakar takardun shaidar ɗan ƙasa biyu wato Nijeriya da ƙasar Guinea. Sannan ta yi watsi da iƙirarin cewa kotu ta tava kama Tinubu da laifin safarar ƙwaya a Amurka.

Mai shari’a Tsammani ya buga misali da shaidar da ayarin lauyoyin Tinubu ya gabatar na wata wasiƙa daga ofishin jakadancin Amurka da ke tabbatar da rashin tarihin aikata laifi na Tinubu a Amurka.

Babu hujja kan iƙirarin aringizon ƙuri’u – Kotu

Mai shari’a Tsammani ya ce kotun ta qi amincewa da iqirarin masu ƙorafi na cewa an yi aringizon ƙuri’u a jihohi irinsu Yobe da Oyo da Kano da sauransu, saboda ba su gabatar da bayani a kan tasoshin zaɓen da al’amarin ya faru ba.

“Hankali ba zai ɗauka ba cewa, mai qorafi ya yi zargin maguɗi a wurare masu yawa cikin tasoshin zaɓe 176,000 da mazaɓu sama da 8000 na qananan hukumomi 774 a cikin jiha 36 da kuma Abuja, amma ba tare da ya zayyana takamaimai wuraren da aka yi maguɗin da ya yi zargi ba,” kotun ta ce.

Hukuncin ya kuma ce jam’iyyar LP ta gaza kafa hujja kan iƙirarin da ta yi, na samun kura-kurai a zaɓen watan Fabrairu.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa Hukumar Zaɓe ta INEC ta rage mata ƙuri’un da ta ci, inda ta ƙara a kan ƙuri’un jam’iyyar APC, sai dai a cewar kotun, jam’iyyar LP ta gaza gabatar da cikakken bayani a kan haƙiƙanin yawan ƙuri’un da ta ci, kafin a rage mata su, kamar yadda ta yi iƙirari, kuma ba su iya ba da bayani a kan tashoshin zaɓen da hakan ta faru ba.

Sai dai, kotun ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta da hurumin ƙalubalantar matsayin Peter Obi na kasancewarsa, ɗan jam’iyyar LP.

APC da Bola Tinubu a cikin ƙorafe-ƙorafensu sun ce babu sunan Obi a rijistar jam’iyyar LP, da aka gabatar wa hukumar zaɓe ranar 25 ga watan Afrilun 2022, abin da suka ce ya saba wa dokar zaɓe ta 2022.

Kotun ta ce ba ta amince da ƙorafin da jam’iyyar LP ta yi na cewa an taɓa tuhumar Bola Tinubu a kan safarar ƙwaya a Amurka ba.

Kuma Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun cancanci tsaya wa takara a zaɓen watan Fabrairu.

Mai shari’a Haruna Tsammani ya ce kotun ta kori ƙorafin da Peter Obi da jam’iyyar LP na cewa sai ɗan takara ya samu kashi 25 cikin 100, kafin a ayyana cewa ya lashe zaben shugaban ƙasa. Kotun ta ce mazaunan Abuja, ba su da wata alfarma ta musamman kamar yadda masu ƙorafin suka yi iƙirari.

Kotun ta kori ƙarar jam’iyyar APM

Tun faro, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Nijeriya, ta yi watsi da ƙarar da ke neman a soke cancantar Kashim Shettima, a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Mai shari’a Haruna Tsammani ne ya tabbatar da haka lokacin da yake karanto hukunci a kan ƙorafe-ƙorafen jam’iyyar APM, da ke ƙalubalantar zaɓen Bola Ahmed Tinubu na APC.

Kotun dai ta ce ta kori matakin ƙalubalantar cewa an ba da sunan Kashim Shettima, don zama ɗan takara har sau biyu ba.

Jam’iyyar APM ta ƙalubalanci matakin ba da sunan Shettima ne a matsayin ɗan takarar sanata a jihar Borno, kafin a sake bayar da sunansa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC.

Tun farko, kotun ta kori ƙorafin APM da ke neman soke cancantar tsayawa takara ga Bola Tinubu da Kashim Shettima.

Hukumomi sun ce sun ɗauki matakai don tabbatar da doka da oda a lokacin sanar da hukuncin da kuma bayan hakan. ‘Yan sanda sun ce sun ƙara tura jami’ansu sassan Nijeriya don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Cikin amo mai ƙarfi, rundunar ‘yan sanda ta ja hankalin waɗanda ta kira ‘yan jamhuru da jiga-jigan siyasa, a kan su yi hattara wajen furta kalamai da ayyukansu, don kuwa ba za ta lamunci iza wutar tarzoma ko abin da zai jefa ƙasar cikin zaman kara zube ba.

Masharhanta na cewa ba a taɓa soke zaben shugaban ƙasa a tarihin Nijeriya ba, tun bayan komawar ƙasar tafarkin dimokraɗiyya a 1999.

Sai dai, ga alama hakan ba shi da wani tasiri a dimokraɗiyya da ke ƙara ƙarfi da haɓaka kamar ta Nijeriya. A 2015, Muhammadu Buhari ya kafa tarihi irinsa na farko a ƙasar, inda ya kayar da shugaban ƙasa mai ci, Goodluck Jonathan.

Alƙalan kotun na gabatar da hukunce-hukuncen ne bayan kwashe tsawon fiye da wata huɗu suna sauraron bahasi da muhawara.

Hukunce-hukuncen da kotun ta ce za ta bayyana kai tsaye ta kafar talbijin “don yin komai cikin gaskiya, ba tare da rufa-rufa ba,” na da matuƙar muhimmanci ga makomar siyasar Nijeriya.

A baya dai, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar nuna zaman kotun kai tsaye ta talbijin.

Har yanzu, zaɓen, ɗaya daga cikin mafiya zafi da Nijeriya ta gani, kuma da aka fi fafatawa tsakanin manyan ‘yan takarar uku, bai daina tayar da ƙura ba, da janyo muhawara musamman tsakanin magoya baya a shafukan sada zumunta.

Hukuncin kotun na zuwa ne daidai lokacin da Bola Tinubu yake cika kwana 100 da hawa mulki. Hukumar Zave ta Nijeriya (INEC) ta ce ya ci zaɓen watan Fabrairu, da yawan ƙuri’a 8,794,726.

Manyan abokan takararsa sun ce ba su yarda ba, kowannensu na cewa shi ne ya yi nasara, don haka shi ya fi cancanta da halarcin zama shugaban Nijeriya.

Akwai damar ɗaukaka ƙara

Masana shari’a a ƙasar kamar fitaccen lauyan Nijeriyar nan, Femi Falana mai lambar SAN na cewa yankan baya da razanarwar da ake yi wa vangaren shari’a irin wanda ba a taba gani ba game da hukuncin kotu, abu ne da ba shi da wata ma’ana.

Ya ce duk ɓangaren da bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba, to yana da damar faukaka ƙara a gaban Kotun Ƙolin Nijeriya.

Yayin hira da gidan talbijin na Channels TV, Femi Falana ya ce ya damu a kan yadda mutane suke nuna cewa komai ya ƙare a sauraron ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa.

A cewarsa, hakan ba gaskiya ba ne. Duk ɓangaren da bai yi nasara ba, kuma ya ji bai gamsu da hukuncin ba, to yana da damar garzaya wa gaban Kotun Ƙoli.

Buhari ya tsomo baki:

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen Sugaban Ƙasa ta yanke na tabbatar da nasarar Jam’iyyar All Progressives Congress da ɗan takararta, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce PEPC ta kafa tarihi ta hanyar yin watsi da tursasawa da duk wani nau’i na son zuciya don tabbatar da adalci bisa doka ga yawancin ‘yan ƙasar da burinsu shi ne a mutunta zaɓin da suka yi.

Idan wani ya ci nasara a yau dimokurafiyya ne da kuma jama’a in ji Buhari saboda haka hukuncin Kotun Ƙoli, lokacin zaɓe ya ƙare kuma lokaci ya yi da za a saka zafi da ƙura a baya.

Daga nan ya kamata sabuwar gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta samu goyon bayan kowa domin cika alƙawuran da ya fauka wa jama’a.

Tsohon shugaban qasar ya kuma bayyana jin daɗinsa ga ɗaukacin ‘yan ƙasa kan yadda suke wanzar da zaman lafiya a tsawon wannan lokaci tare da addu’ar samun ci gaba da ci gaba a gwamnatin APC.

Ya kuma miqa saƙon taya murna ga Shugaban Ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa da jam’iyyar All Progressives Congress bisa nasarar da suka samu a kotu, yana mai nuna musu fatan alheri a gare su wajen ganin sun cika burin al’umma da suka ɗauka tunda farko a yayin yaƙin neman zaɓen da suka gudanar a faɗin ƙasa.

Ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su tabbatar sun goyi bayan wannan jaririyar gwamnatin wajen ganin an kai ga samun nasarar gudanar da ayyuka na alheri da aka soma gudanarwa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Tinubu ya nuna gwanintar mulki a kwana 100 – Ministan Labarai

A yayin da Kotun Zaɓe ke yanke hukuncinta, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya, Muhammed Idris Malagi, ya bayyana cewa, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya cika kwanaki 100 akan karagar mulki, inda Nijeriya ta samu cigaba da kuma farfaɗowa.

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa domin cika kwanaki 100 na Shugaban ƙasar a matsayin Shugaban Nijeriya.

A cewarsa, a cikin wannan lokaci, shugaban ƙasar ya nuna ƙwarin gwiwa da jajircewa wajen cire tallafin man fetur domin kaucewa bala’in tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce: “Taimakon masu ƙarfi ne da ake yi ta hanyar biyan tallafin man fetur ya rataya a kan Nijeriya shekaru da dama. Hakan ya kawo cikas ga ci gaban ƙasar kuma ya sanya ƙasar ta zama cikin rance.”

“Bugu da ƙari cire tallafin, Shugaba Tinubu ya ƙara ɗaukar matakai na haɗa kan kasuwannin canji da dama.

“Yayin da waɗannan muhimman matakai guda biyu na ceto ƙasar nan daga tavarvarewar sun kawo wa ‘yan Nijeriya rashin jin daɗi na wani ɗan lokaci, Shugaba Tinubu bai tava kasa yin ƙasa a gwiwa ba wajen kira ga ‘yan Nijeriya da su ga irin matsalolin da ake fama da su a halin yanzu a matsayin farashin da ya kamata mu biya domin ceto ƙasarmu daga rugujewa,” Ministan ya ƙara da cewa.

A dai dai kwanaki 100 da suka gabata ne Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya hau karagar mulki biyo bayan wa’adin da al’ummar Nijeriya suka yi masa na alheri, waɗanda suka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasarmu na 16.

Tun a ranar 29 ga watan Mayu, Shugaba Tinubu ke kan muƙaminsa, yana aiki tuƙuru don cika alƙawuran yaƙin neman zaɓenda kamar yadda aka bayyana a cikin Ajandar sa na sabunta fata don ci gaban Nijeriya.

Ministan ya ce shugaban ya fara tafiya ne domin sake gina tattalin arzikinmu da ya durƙushe, ganin cewa ƙasarmu na cikin wani mawuyacin hali na basussukan da muke bin al’umma na gida da waje tare da tsarin tallafin man fetur da ba zai ɗore ba, wanda ya haifar da ruɗani a cikin al’ummarmu tsawon shekaru da dama, kuɗi, wanda ya mayar da matakai uku na gwamnatoci ba su da matsala kuma ba su iya biyan buƙatun ‘yan ƙasa.

“Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin jajircewa da wajen cire tallafin man fetur domin kaucewa bala’in tattalin arzikin ƙasa mai girman gaske.

“Baya ga cire tallafin, Shugaba Tinubu ya ƙara ɗaukar matakai na haɗa kan kasuwannin canji da dama.

“Bisa la’akari da raɗaɗin da jama’a ke ji, gwamnati ta fitar da shirye-shiryen shiga tsakani don taimakawa wajen rage raɗaɗin cire tallafin. Waɗannan ayyukan sun haɗa da samar da mafi ƙarancin albashi da ƙarin albashi, tallafawa jihohi da ƙananan hukumomi don ba su damar ciyar da marasa galihu a cikinmu, samar da takin zamani ga manoma, hatsi ga gidaje, raba kuɗaɗe ga masu ƙaramin ƙarfi. Baya ga waɗannan, akwai shirin samar da motocin bas masu amfani da gas na CNG sama da 11,000 don zirga-zirgar jama’a da dai sauransu.”

Mohammed Idris ya ci gaba da cewa: “Yayin da yake ƙoƙarin rage tasirin tsadar rayuwa ga ’yan ƙasa, Shugaba Tinubu ya mayar da hankali ne wajen karkatar da tattalin arzikinmu tare da kawar da duk wani cikas ga samar da fa’ida ta yadda ɓangaren zai bunƙasa da samar da miliyoyin ayyukan yi masu inganci da ci gaban tattalin arziki.

“A cikin kwanaki 100 da suka gabata, gwamnati ta kafa kwamitin sake fasalin haraji da kasafin kuɗi wanda ke kan aikin zurfafa gyare-gyaren da ake yi da kuma sake fasalin tattalin arzikin ƙasa don ɗorewa zuwa dogon lokaci. Shahararren kwararre kan manufofin Haraji da Kudi ne ke jagorantar wannan kwamiti. Wani vangare na wa’adin kwamitin, aiki tare da gwamnatocin jihohi, shine sauƙaƙa tsarin harajin mu mai sarƙaƙiya, kawar da haraji da yawa, daidaita ƙa’idoji waɗanda ke hana sauqin yin kasuwanci, da kuma cike giɓin haraji sama da tiriliyan 20 na shekara.

“Don tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya da ‘yan kasuwa ba su da nauyi a kan sabbin haraji, gwamnati za ta inganta yadda ya dace wajen tattara kuɗaɗen shiga. Za ta faɗaɗa hanyar biyan haraji ta hanyar tabbatar da cewa an sanya waɗanda ba su biya ba su biya yayin da waɗanda ba su biya daidai ba an sanya su su biya nasu kason,” inji shi.

Malagi ya ce, a cikin kwanaki 100 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya yi ƙoƙarin inganta siyasar Nijeriya domin ya fahimci cewa ba za a samu wani ci gaba mai ma’ana da ci gaba ba idan ba zaman lafiya ba.

Ya ce gwamnati ta daidaita harkokin siyasa tare da rage tashe-tashen hankula da ke da nasaba da rikicin ƙabilanci da na addini ta hanyar kula da bambance-bambancen mu. Shugaba Tinubu ya yi imanin cewa bambancin Nijeriya wani ƙarfi ne na yin amfani da shi don ci gaban ƙasa. Domin ƙarfafa danƙon haɗin kan ƙasa da zamantakewar al’umma, Shugaba Tinubu ya tabbatar da daidaito a dukkan naɗe-naɗen muƙamai a manyan muƙaman gwamnati ciki har da na shugabannin ayyuka daga sassa daban-daban na ƙasar.

Haka zalika, ya ce yayin da ake inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali na siyasa a cikin ƙasar ta hanyar ɗaukar kowane ɓangare na ƙasarmu, shugaban ya kuma ba da fifiko ga isassun bayanai game da ayyukan gwamnati da manufofin gwamnati. Shugaba Tinubu ya zama Shugaban Ƙungiyar ECOWAS a cikin kwanaki 100 da ya yi yana mulki.

Malagi ya ce “A cikin wannan rawar da ya taka, ya yaba wa Nijeriya a duniya da ma na yankin Yammacin Afirka, wajen inganta tsarin doka, da kare tsarin mulkin ƙasa, da tsayawa tsayin daka wajen yaƙi da kutsen da sojoji suka yi a harkokin mulki, musamman a Jamhuriyar Nijar, inda aka kifar da gwamnatin dimokaraɗiyya kwanan nan.

“Ba baka kawai ba ne Nijeriya ke ci gaba da samun karramawa daga sauran ƙasashen duniya. Hakan ya faru ne saboda tsayin daka da ƙa’ida ta Shugaba Tinubu na aƙidar dimokuraɗiyya da bin doka da oda da shugabanci na gari.”

Ministan ya kuma ce a ci gaba da yunƙurin Tinubu na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, shugaban ya yi tattaki zuwa ƙasar Indiya tare da rakiyar wasu zaɓaɓɓun ministoci da kuma ‘yan kasuwa sama da 30 na sassan tattalin arziki daban-daban domin halartar taron G20, inda ya ce wannan yunƙurin ya nuna shirye-shiryen Nijeriya masu ma’ana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *