Bayan kwana 38 a hannun ‘yan bindiga, Ameerah ‘yar Dr Ramatu Abarshi ta shaƙi iskar ‘yanci

Daga WAKILINMU

Ameerah, ɗiyar Dakta Ramatu Abarshi, malama a Kwalejin Fasaha ta Kaduna ta kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da ita.

Jaridar Daily Trust ta ruawaito cewa, an yi garkuwa da Dakta Abarshi da ‘yarta da kuma direbansu Ibrahim ne a ranar 24 ga Afrilu, 2022, a Babbar Hanyar Kachia zuwa Kaduna sa’ilin da suke dawowa daga aikin tallafa wa masara galihu.

Masu garkuwar sun sako Abarshi ne kimanin makonni uku da suka gabata, direban nasu a makon da ya gabata, sai ‘yar wadda aka sako ta kwanaki biyar bayan sako direban.

Majiya ta kusa da waɗanda lamarin ya shafa ta ce, “Lallai an sako Ameerah ranar Talata da yamma. Ta haɗu da iyayenta kafin aka ɗauke ta zuwa wani asibiti don duba lafiyarta.

“Lamarin ba mai sauƙi ba ne, amma duk da haka mun gode wa Allah ta dawo gida,” inji majiyar.

Bayanai sun nuna sai da aka biya fansa na miliyoyin Naira kafin aka sako Ameerah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *