Bayan rantsuwa, Trump ya ɗauki gagarumin mataki

Daga USMAN KAROFI

A ranar farko da Donald Trump ya hau kan mulki a matsayin Shugaban Amurka, gwamnatinsa ta sanar da rufe manhajar CBP One, wacce gwamnatin Biden ta ƙirƙiro don bayar da damar neman mafaka cikin tsari ga ‘yan gudun hijira da ke shirin shiga Amurka ta iyakar kudu.

Manhajar CBP One ta taimaka wajen rage yawan shiga ba bisa ƙa’ida ba a iyakar kudu ƙarƙashin gwamnatin Biden, inda ta baiwa kusan mutane miliyan ɗaya damar shiga Amurka ta hanyar shige da fice na doka. Sai dai, a yanzu, hukumar U.S. Customs da Border Protection (CBP) ta bayyana cewa duk ayyukan manhajar da suka haɗa da bayar da bayanai na farko da tsara lokacin shiga sun daina aiki daga 20 ga Janairu, 2025, tare da soke dukkan tsare-tsaren da aka yi a baya.

Gwamnatin Trump ta bayyana cewa wannan matakin na daga cikin sabbin tsare-tsarenta don tsaurara matakan shige da fice da kuma tabbatar da bin doka wajen neman mafaka a Amurka. Wannan ya biyo bayan rahoton hukumar CBP cewa watan Nuwamba 2024 ne ya samu mafi ƙarancin yawan shiga ba bisa ƙa’ida ba ƙarƙashin mulkin Biden.