Bayan sama da wata bakwai: ASUU za ta janye yajin aiki nan ba da daɗewa ba – Osodeke

Daga BASHIR ISAH

Ɗaliban jami’o’in gwamnati a faɗin Nijeriya na ci gaba da nuna farin cikinsu bayan da yajin aikin da malamansu suka yi ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ASUU ya zo ƙarshe.

Kimanin watanni takwas aka shafe ASUU na yajin aiki inda sai a kwanan nan lamarin ya zo ƙarshe bisa umarnin kotu ga ƙungiyar.

Bayan tirka-tikar da aka yi tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya, ƙungiyar ta ba da sanarwa a ranar Talata cewa za ta janye yajin aikin nata nan ba da daɗewa ba.

A ranar Litinin malaman jami’o’in suka bayyana cewa, suna da yaƙin shiga tsakani da Majalisar Wakilai ta yi hakan zai haifar da ɗa mai ido.

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce akwai haske a tattaunawar da suka yi da Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, kan batun yajin aikin nasu.

Malaman da lamarin ya shafa sun shiga yajin aiki ne domin neman haƙƙoƙinsu da suka maƙale a wajen Gwamnatin Tarayya.

Tun a ranar 14 ga Fabrairun 2022 ASUU ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani kan sai gwamnatin ta cimma buƙatunta kafin ta janye yajin aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *