Bayan shafe sa’o’i uku a kan layi, Gwamna El-Rufai ya kaɗa ƙuri’arsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Bayan haƙuri a kan layi na tsawon lokaci, gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sauke nayinsa na jama’a a mazaɓarsa na PU024 da ke Unguwar Sarki GRA a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa.

Da yake magana da manema labarai bayan kaɗa ƙuri’arsa, El-Rufai ya ce, ana neman masu kaɗa ƙuri’a a yankin Kudancin Kaduna da su zaɓi wata jam’iyya ko kuma su koma gidajensu.

Ya ce, a halin yanzu jami’an tsaro na gudanar da bincike a jihar.

Gwamnan ya ce, an gudanar da zaɓen a wasu rumfunan zaɓe ba tare da wata matsala ba.

“Babu komai, babu matsala, babu wata matsala, tsarin tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) ya tantance ni da amfani da na’urarar, komai ya faru ba tare da wata matsala ba, kuma an buɗe rumfar zaɓe da ƙarfe 8 na safe,” inji shi.

“Gaba ɗaya tsarin yana tafiya lafiya a faɗin jihar, sai dai a wasu wurare a kudancin Kaduna an samu rahoton tursasa masu kaɗa ƙuri’a inda ake neman jama’a su zaɓi jam’iyya ɗaya ko kuma su koma gida kuma jami’an tsaro na ci gaba da bincike.

“Mun yi tsammanin za a iya samun tashin hankali amma cikin ikon Allah ba a samu wani rahoto na hakan ba, kuma an samar da ingantaccen tsarin tsaro domin mayar da martani ga wannan bayanan. Kuma ya zuwa ana samun cigaba, ina fatan mutane da yawa su fito, har yanzu yawan masu jefa ƙuri’a ya ragu kaɗan, amma muna da kyakkyawan fata.”

A halin da ake ciki, jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito El-Rufai ya kaɗa ƙuri’arsa ne da misalin ƙarfe 11:45 na safe a mazaɓarsa mai lamba 024, Unguwan Sarki GRA, a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa.

Gwamnan Kaduna yana kammala wa’adinsa na biyu a ofis kuma yana goyon bayan takarar Uba Sani, ɗan takarar jam’iyyar PPC.

A jihar, jam’iyyar mai mulki ta sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya ga jam’iyyar adawa ta PDP.