Bayan shekara 10, New Zealand na jimamin girgizar ƙasar da ta fuskanta

Daga WAKILIN MU

A wannan Litinin ne Ƙasar New Zealand ke cika sheka 10 da faruwar ibtila’in girgizar ƙasa da ya auku a birnin Christchurch wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 185, tare da jikkata wasu dubbai.

Girgizar ƙasar wadda ta kai ƙarfin maki 6.3 da zurfin kilomita 5, ta faru ne a ranar 22, Fabrairu, 2011.

Domin tuna zagayowar wannan rana, ɗaruruwan ‘yan ƙasar ne suka taru a wani wajen taro a birnin Christchurch domin tunawa da duka waɗanda suka rasa rayukansu a wancan lokaci.

Haka nan, an ga yadda aka yi ƙasa-ƙasa da tutoci a sassan ƙasar domin nuna alhinin rashe-rashen da girgizar kasar ta haifar shekaru goma da suka gabata.

Firam Ministan ƙasar, Jacinda Ardern, ya ce yanzu lokaci ne da za a duba yadda makomar birnin zai kasance a gaba, birnin da shi ne gari mafi girma na biyu a ƙasar New Zealand.

Kimanin mutum 87 da suka mutu a girgizar ƙasar baƙi ne daga wasu ƙasashe, da suka haɗa da Chaina da Japan da Australia da dai sauransu.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*