Daga WAKILINMU
Shekaru 28 bayan da Gwamnatin Tarayya ta yi wa ‘yan wasan Super Eagles alƙawarin gidaje kyauta, sai a wannan karon Shugaba Muhammadu Buhari ya cika wannan alƙawari da gwamnatocin baya suka kasa cikawa.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaba Buhari da kansa a lokacin da ya ke ƙaddamar da sababbin gidaje da gwamnatinsa ta gina a Lafiya, Babban Birnin Jihar Nasarawa a ƙarshen makon jiya, yana mai cewa, gwamnatinsa a shirye ta ke wajen saka wa duk ɗan ƙasar da ya yi aiki tuƙuru wajen gina Nijeriya.
Idan dai za a iya tunawa, a 1994 Gwamnatin Nijeriya ta yi wa ‘yan wasan da suka lashe Gasar Kofin Afrika da aka gudanar a Ƙasar Tunisiya, inda cika wannan alƙawari a yanzu ya gwada yadda Gwamnatin Shugaba Buhari ke ƙoƙarin dawo da karsashin ‘yan wasan Nijeriya a kowane mataki.