Bayan shekaru 40 da gano cutar ƙanjamau masana sun kasa samar da maganinta

Daga WAKILINMU

A ranar Labara da ta gabata duniya ta yi bikin ranar yaƙi da cutar ƙanjamau a wani yanayi cike da fatan lalubo maganin cutar bayan shafe shekaru 40 da gano ta amma ba tare da magani ko kuma rigakafinta ba, sai dai ɗan cigaban da aka samu na samar da ƙwayoyin rage tasirinta a jikin masu ɗauke da ita.

Yunƙurin yaƙar cutar da Majalisar Ɗinkin Duniya ke yi ƙarƙashin shirin UNAIDS cike da fatar samar da maganin na ƙanjamau kafin shekarar 2030 ya ci karo da babban ƙalubale bayan bullar cutar Korona da ta kawo tangarɗa a yaƙi da kusan dukkanin cutuka masu haɗari.

Tun daga shekarar 1988 ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware kowacce ranar 1 ga watan Disamba don yaƙi da cutar ta Ƙanjamau da kuma wayar da kai game da illarta bayan da ta shiga jerin cutuka mafiya haɗari da ke kisa ba ƙaƙƙautawa.

A shekarar 1981 ne aka faro ganin yanayin cutar jikin wasu masu auren jinsi a California amma sai tsakiyar 1982 aka tantance cutar tare da bata suna, yayin da a shekarar 1983 aka gano ƙwayar cutar da ke haddasa Ƙanjamau ɗin wato HIV.

Shekaru bayan gano ƙwayar cutar ne masana a Amurka maƙyanƙyasar cutar suka samar da magunguna rage kaifinta da aka yiwa laƙabi da AZT a shekarar 1988 lokacin ana da mutum 150,000 jumullar masu ɗauke da cutar ta Ƙanjamau a duniya bakiɗaya, kuma a wancan lokaci ne aka fara wayar da kai a ƙoƙarin yaƙarta la’akari da yadda ta ke fantsamuwa.

Daga shekarun 1990 ne aka fara samun mutuwa sanadiyyar cutar kuma mutum na farko da ta kashe shi ne jarumin Amurka Rock Hudson kana mawaƙiyar Birtaniya Freddie Marcury da kuma Rudolf Nureyev ɗan rawa daga Rasha.

A shekarun 1994 cutar ta Sida ko ince Ƙanjamau ta zama mafi kisa ga matasan Amurka galibi waɗanda shekarunsu ya fara daga 25 zuwa 44 gabanin 1996 da ƙasar ta yi nasarar samun raguwar masu ɗauke da cutar.

Daga shekarun 1999 ne jumullar masu ɗauke da cutar ya kai miliyan 50 a sassan duniya yayin da ake samun qaruwar mace-mace bayan rasa rayukan mutane miliyan 16 la’akari da tsadar ƙwayoyin rage kaifinta da Amurka ta samar.

Alƙaluman WHO na nuna cewa har yanzu nahiyar Afrika ke kan gaba a jerin yankunan da ke da yawan masu fama da wannan cuta ta HIV tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu.

Wani rahoton UNAIDS ya koka da yadda kashi 2 bisa 3 na masu ɗauke da cutar ke rayuwa ta hanyar dogaro da magungunan rage kaifin cutar.

Alƙaluman UNAIDS ya nuna cewa cikin shekaru 40 bayan vullar cutar ta Sida ta hallaka mutane miliyan 36, 300,000.