Bayan shekaru biyu, huɗu daga ‘yan matan Yauri sun shaƙi iskar ‘yanci

*Janar Abdulsalam da Malami na daga cikin waɗanda suka ba da gudunmawa na miliyoyin Naira

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga Jihar Kebbi sun ce huɗu daga cikin ɗaliba 11 na Sakandaren Gwamnati da ke Birnin Yauri Jihar Kebbi da suka rage a hannun ‘yan bindiga sun shaƙi iskar ‘yanci.

Manhaja ta gano cewa Bilha Musa da Faiza Ahmed da Rahma Abdullahi da kuma Hafsa Murtala, su ne waɗanda suka kuɓuta daga hannun gawurtaccen ɗan fashin dajin nan, Dogo Gide, da yammaxin ranar Juma’a

Munira Bala Ngadski da Sarah Musa na daga cikin iyayen ɗaliban hudu da suka shaki iskar ‘yanci, sun bayyana farin cikinsu tare da yin godiya ga Allah. Sai dai a cewar Sarah Musa har yanzu suna cike da juyayi a kan sauran ɗalibai bakwai da har yanzu ke cikin daji a hannun ‘yan bindiga kusan shekara biyu.

Ta ƙara da cewa, wasu daga cikinsu, ko da Allah ya yi fitowarsu ba za su taras da mahaifansu ba saboda baƙin cikin rashin yaran ya yi ajalinsu.

A ranar 17 ga watan Yuni na 2021 ne masu garkuwa da mutane suka afka Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya da ke birnin Yauri, Jihar Kebbi suka sace ɗalibai da malamai da wasu ma’aikatan makarantar.

Bayan da gwamnati ta ceto wasu daga cikin ɗaliban da aka sace har sau biyo, an samu ragowar ɗalibai mata 11 a hannun ‘yan bindigar.

Iyayen yaran sun yi ta jerangiya tare da neman taimakon hukumomi don ceto sauran ɗaliban amma haƙarsu ta gagara cimma ruwa, har sai da suka ƙaddamar da neman taimakon kuɗin biyan fansa daga jama’a.

Salim Ka’oje, shi ne ya jagoranci wannan fafutuka, ya ce lamarin ya kai ga sayar kaddarori da gonakinsu suka haɗa da kuɗin da jama’a suka tattara don ceto yaran.

Ya kara da cewa wani kwamiti mai mambobi biyar wanda ya jagoranta ne ya yi shahada tare da shiga dajin don neman ceto ɗaliban.

Duk da yake Gwamnatin Kebbi ba ta taka wata muhimmiyar rawa wajen ceto ɗaliban ba, a yanzu dai gwamnatin ce ke ɗaukar nauyin kula da lafiyar ɗaliban da suka shafe shakara biyu a daji, a cewar shugaban Ƙungiyar Iyayen Yaran, Salim Argungu.

A halin da ake ciki, Salim ya ce suna ci gaba da fafutukar ganin an sako sauran ‘yan mata bakwai da suka rage a hannun ‘yan bindigar.

Da ya taɓo batun yayin huɗubarsa ta ranar Juma’a, Babban Limamin Birnin Yauri, Sheikh Muhammad Ibrahim, ya ce ana gab da kuɓutar da ragowar ‘yan matan sakamakon wasu bayin Allah sun cikasa miliyan N105 da ake buƙata don kuɓutar ɗaliban.

A cewar limamin Janar AbdulSalami Abubakar ya ba da gudunmawar miliyan N5, Babban Lauyan Ƙasa, Malami SAN, ya ba da miliyan N10, Janar Aminu Bande (mai ritaya), wanda ya kasance ɗan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a jihar, miliyan N3, Sanata Adamu Aleiro miliyan N6, Malamawan Kebbi miliyan N5, da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *