Bayan shekaru tara, Jonathan ya yi tsokaci game da faɗuwarsa a zaɓen 2015

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi tsokaci game da faɗuwarsa zaɓen shekarar 2015, inda ya bayyana hakan a matsayin lokaci mai tsanani ga harkar siyasarsa.

Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana irin yadda zuciyarsa ta kaɗu a lokacin da ji sakamakon zaɓen kasancewar ya na ji kamar baki ɗaya duniyar na ƙin sa ne.

Jonathan ya faɗi hakan ne a Abuja yayin Lekcar tunawa da Raymond Dokpesi wanda Hukumar gudanarwa ta Daar Communications ta shirya tare da haɗin-gwiwar Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Ƙasa.

Jonathan ya tsaya takarar shugaban ƙasa ne a ƙarƙashin jami’yyar PDP a 2015 inda Muhammadu Buhari na jami’yyar APC ya doke shi.

Buhari ya samu ƙuri’u 15,424,921 inda Jonathan kuma ya yi rashin nasara da ƙuri’u 12,852,162 a matsayi na biyu wanda hakan ya sa ya zamo shugaba mai ci na farko da ya rasa damar koma wa kujerarsa Nijeriya.

Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Bayelsan ya kuma yaba da irin muhimmiyar rawar da tsohon shugaban Daar Communications, marigayi Raymond Dokpesi ya taka kafin ya bai wa Buhari ragamar mulkin Nijeriya.