Bayan wani mahaukacin ɗan bindiga sai mahaukaciyar ƙasa

Daga CMG HAUSA

A yayin da mutane suka je kasuwa don sayen kayayyaki a ƙarshen mako, ba su san hawa ba balle sauke, sai kawai aka harbe su da bindiga. Wannan harin da ya abku ba gaira ba dalili shi ne abin da ake kira “hauka”.

Wani saurayi farar fata mai shekaru 18 a duniya ne, ya ƙaddamar da wannan hari a ranar Asabar da ta wuce, a wata kasuwar zamani dake garin Buffalo na jihar New York ta ƙasar Amurka. Inda ya rika watsa hotunan bidiyon yadda yake kashe mutane kai tsaye a shafin yanar gizo. Cikin ‘yan mintuna aka ga wasu mutane 13 sun fadi ƙasa. Cikinsu 10 sun mutu, waɗanda dukkansu baƙaƙen fata ne.

Kafofin watsa labaru na ƙasar Amurka sun ce, saurayin ya sanya tambari mai siffar “bakar rana” a jikin rigarsa, wanda ya kasance alamar ‘yan Nazi, kuma irin tambarin da sojojin bataliyar Azov ta ƙasar Ukraine suka sanya. Ban da wannan kuma saurayin ya watsa wata doguwar sanarwa mai shafuka 180 a shafin yanar gizo, inda ya ce baƙaƙen fata “ ba mutane ba ne”. Maganar dake nuna ra’ayin fararen fata masu tsattsauran ra’ayi.

Wannan tunani ne na mahaukata, amma ruwa ba ya tsami banza. Tun tuni ƙasar Amurka ta fara nuna goyon baya ga ƙungiyoyin ƙasar Ukraine masu adawa da ƙasar Rasha, ciki har da bataliyar Azov, mai aƙidar Nazi da ra’ayi na fararen fata sun fi sauran al’ummun duniya. Sai dai munafuncin dodo ya kan ci mai shi, yanzu ƙasar Amurka ita ma ta fuskanci aƙidar ‘yan Nazi, kana ra’ayi na nuna bambancin launin fata ya haddasa ɗimbin matsaloli a ƙasar.

Sai dai ƙasar Amurka ba ta lura da matsalolin sosai ba. Ko da yake bambancin launin fata da ƙabilanci sun haddasa hasarorin rayuka masu tarin yawa a ƙasar, kana yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha ya yi tasiri kan tsarin samar da kayayyaki na ƙasar Amurka, da haddasa matsalolin tattalin arziki, kamar ƙarancin garin madarar jarirai a ƙasar.

Ban da wannan kuma, wasu ƙwararru sun ce dimbin makamai da ƙasar Amurka ta ba ƙasar Ukraine a matsayin tallafi, za su iya shiga hannun ‘yan ta’adda, da haddasa rigingimu a duniya.

Duk da haka, kasar Amurka na ci gaba da ƙoƙarin samar da makamai ga ƙasar Ukraine, kana tana shirin zartas da ƙudurin samar da karin tallafi da darajarsa ta kai dala biliyan 40 ga ƙasar Ukraine.

Haƙiƙa ƙasar Amurka ba ta son ganin kura ta lafa a ƙasar Ukraine, ko da yake yakin da ake yi a can, ba zai haifar da da mai ido ga daukacin al’ummar duniya ba.

Hakan na nuna mana cewa, manufofin ƙasar Amurka sun sa aka samu wannan mahaukacin dan bindiga farar fata. Haƙiƙa, ita ma mahaukaciya ce, wato ƙasar Amurka.

Mai Fassara: Bello Wang

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *