Bayern Munich ta daƙile burin PSG na lashe gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Bayern Munich ta kawo ƙarshen fatan PSG na lashe kofin zakarun Turai cikin wannan kaka, bayan da ta lallasata da ƙwallaye biyu da nema a wasansu na daren ranar Laraba.

Tun a haɗuwar farko dama Bayern Munich ta lallasa PSG da ƙwallo 1 mai ban haushi har gidanta cikin watan jiya, gabanin nasarar ta daren ranar wanda ke nuna tauraruwar ta Jamus ta doke zakarar ta Faransa da ƙwallaye 3 da nema a jumlace.

Cikin shekaru 11 da PSG ta shafe ta na fafutukar ganin ta lashe kofin na zakarun Turai, wannan ne karo na biyu a jere da ake cire ƙungiyar a matakin zagaye na biyu a gasar kuma karo 5 a cikin shekaru 7.

’Yan wasan ƙungiyar Kylian Mbappe da Lionel Messi basu taka rawar ganin da aka saran za su taka yayin wasan na Laraba ba lamarin da ya ja musu kakkausar suka musamman Messi wanda ƙungiyar ta zuba maƙudan kuɗi wajen sayenshi don ganin ya kawo mata kofin na zakarun Turai.

Sai dai anga yadda Sergio Ramos yayi ƙoƙarin dawo da PSG a wasan na Laraba yayin wasu hare-hare biyu da ya kai amma yunƙurin na sa ya ci tura.

Tsohon ɗan wasan Ingila Owen Hargreaves da ke sharhi kan wasan na jiya, ya ce abin kunya ne yadda PSG ta tattara tarin matasa kuma zakakuran ’yan wasa masu matuƙar tsada amma a ko da yaushe take ci baya maimakon gaba.

Manajan PSG Christope Galtier ya ce abin takaici ne yadda suka rasa damar kaiwa gaba a gasar ta zakarun Turai amma dole su karɓi gaskiyar cewa sun tamkar kuskure tare da laluben hanyar gyara.

Tun bayanda ’yan kasuwar Ƙatar suka ƙarfi ragamar ƙungiyar ta PSG a shekarar 2012 ta kasha kuɗin da ya haura dala biliyan 1 wajen sauya fasalin ƙungiyar tare da mayar da ita gagarabadau tsakanin takwarorinta inda zuwa yanzu ta lashe kofunan Lig 1 guda 8 sai kofunan kananun gasar cikin 12.

Amma har zuwa yanzu ƙungiyar ta gaza lashe kofin na zakarun Turai, inda suka yi rashin nasara a wasan ƙarshe na kofin gasar a shekarar 2020 a hannun Bayern Munich.