Bayero ya magantu kan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara

Daga BELLO A. BABAJI

A karon farko, Alhaji Aminu Ado Bayero ya magantu kan hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a ranar Juma’ar da ta gabata, inda hukuncin ya nuna cewa, Babbar Kotun Jiha ba ta yi masa adalci ba kan hukuncin da ta yanke game da matsayarsa kan Masarautar Kano.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mataimaka wa Bayero kan harkokin yaɗa labarai, Khalid Uba Adamu, ya ce, “Masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ta nuna godiyarta ga Allah bisa yadda kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin dambarwar masarautar a ranar Juma’a 10 ga Janairu, 2025 inda aka kara tabbatar da mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero har yanzu shine Sarkin Kano.

“Masarautar tace yanke hukuncin da kotun daukaka kara tayi na rushe hukuncin babbar kotun jihar Kano ya kara tabbatar da yadda masu shari’a suke gudanar da aikinsu bisa kwarewa da kuma bin diddigi don kwato hakkin wanda aka zalunta.

“Babu shakka Masarautar kano me biyayya ce ga dukkanin al’amuran da hukunci ya zartar ko ya bayar da umarni ta kuma ƙara jaddada aniyarta nayin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da umarnin da kotun ta yi.

“Masarautar ta Kano ta lura da yadda wasu mutane suke yunkurin juya abinda hukuncin kotun daukaka karar ya kunsa, da kawo rudani ta hanyar nuna cewa sune suka yi nasara.

“Masarautar tayi kira ga al’umar jihar Kano musamman masoya mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero dake ko ina a kasarnan da sassan duniya da su kwantar da hankalinsu, aci gaba da addu’a kasancewar har zuwa wannan lokaci mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero shine halastaccen Sarkin Kano a idon doka da hukumomin shari’a.

“Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya a wannan jiha tamu. Allah ya bamu nasara a sauran matakan shari’a dake gaba.“

Idan za a iya tunawa, a hukuncin na ranar Juma’a, wanda Mai Shari’a Mohammed Mustapha ya jagoranci alƙalai uku, ya kuma rushe hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yi, wacce ta bayar umarni kan tauye haƙƙin bil adama kan Alhaji Aminu Ado Bayero, yana mai cewa, ba ta da hurumin sauraron ƙarar. Amma Alƙali Mustapha ya kuma bayar da umarnin rushe hukuncin Babbar Kotun Jiha, wanda ya sauke Bayero, yana mai cewa, a naɗa sabon alƙalin da zai yi adalci a shari’ar.