Bayyana da yaɗuwar harshen Hausa da Hausawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kamar yadda mu ka faɗa a makon da ya gabata cewa, za mu riqa kawo wa masu karatu tarihin manyan ƙabilun Nijeriya, a yau za mu bayyana taƙaitaccen tarihin asalin Hausawa da harshen Hausa a Nijeriya.

Ƙabilar Hausa dai ƙabilace da ke zaune a Arewa maso Yammacin Tarayyyar Nijeriya da Kudu maso Yammacin Jamhuriyyar Nijar. Ƙabilace mai ɗimbin al’umma, amma kuma a al’adance mai mutuƙar haɗaka, aƙalla akwai sama da mutane miliyan 50 da harshen yake asali gare su. A tarihi an ce, ƙabilar Hausawa na tattare a salsalar manyan birane. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300’s, sannan suka sami nasarori da dauloli kamar su Daular Mali Songhai, Borno da kuma Fulani.

Hausawa wani jinsi ne na jama’a da suka samu kansu mafi yawa a yammacin Afrika, mutane ne da suka kafa garuruwa daban-daban, sannan duk garin da suka kafa suna da jagoranci na sarautarsu.

Ba su samu damar haɗa kansu wuri guda ƙarƙashin tuta ɗaya ba, hakan ya sa ake kiran kowanne da sunan garinsu da kuma sunan sarautarsu. Abin da ya zo ga tarihi, ƙasar Hausa na da manyan garuruwa guda bakwai wato inda suka fara zama, waɗannan garuruwa sun haɗar da Daura da Gobir da Kano da Katsina da Zazzau da Rano da kuma Birom.

A wasu lokutan Hausawa sun sami gagarimin ikon, mulki da haɗaka ta kau da baki ’yan neman ruwa da tsaki, da kuma neman aringizon a cikinta da kuma harƙallar ko cinikin bayi. A farko-farkon shekaru na 1900’s, a lokacin ƙabilar Hausa ke yinƙurin kawar da mulkin aringizo na Fulani, sai turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mamaye arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida, a bisa ƙarƙashen mulkin Birtaniya,’yan mulkin mallaka sai suka marawa Fulani baya na cigaba da manufofin angizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin kafin gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne ya yi kane-kane a arewacin Nijeriya. Wannan haɗakar gamin kambiza, an farota ne tun asali a matsayin fulani su ɗare madafun ikon a tsararren tsarin siyasar arewa.

Akasarin masu mulki na fulani sun kasance yanzu, a al’adance hausawa gwamitse Ko da yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma ya zuwan addinin Islama da kuma karɓansa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bambam. Ginshiƙoƙin al’adun hausawa na da mutuƙar zaranta, kwarewa da sanaiya fiye da sauran al’ummar da ke kewayenta. Sha’anin noma ita ce babbar sana’ar hausawa inda hausawa ke ma sana’ar noma kirari da cewa, na duƙe tsohon ciniki kowa yazo duniya kai yatarar, akwai kuma wasu sana’o’in kamar su sha’anin jima watau harkar fatu, rini, saƙa da ƙira, fannonin da ke mutuƙar samun cigaba a harkokin sana’o’in hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha’anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana.

Harshen Hausa shi ne mafi girma da kuma mafi sanaiyar harshe a nahiyar Afirka, harshen hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman Larabci kana kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa al’adar cuɗeni-na-cuɗeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama’a da ba hausawa bane a nahiyar Afirka. Bugu da ƙari, akwai cincirindon al’ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacinta da kuma yankunan cinikayyar al’ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa aikin hajji.

Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da ƙasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami da aka buga tun kafin zuwan turawa ’yan mulkin mallaka na Birtaniyya. Har ila yau, kuma wani tsarin rubutu a ajami da aka ƙirƙiro tun kafin zuwan turawa, da ba kasafai ake amfani da shi ba yanzu.

To, masu salon Magana kan ce zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai, ko da al’adunsu suka fara cudanya sai kuma sabbin matsaloli suka bijiro, da suka haɗar da yunwa da kuma yaƙe-yaƙe, a nan ne wasunsu suka fara hijira suna kafa wasu garuruwan da kuma sarautunsu, duk inda suka kafa gari sai su naɗa sarautarsu, da dama suna alaƙanta sarautarsu da ita Daura, amma wasu ba su alaƙanta ba.

Alaƙar Hausawa da Bayajidda:
Tarihi ya nuna cewa Bayajidda ya bayyana ne tsakanin ƙarni na 16 zuwa na 19 amma kuma akwai shaidar kasancewarsa a al’adar Hausawa tun cikin ƙarni na 9 zuwa na 10.

Sunansa na asali shi ne Abu Zaid. Amma saboda ba ya jin harshen Hausa sai aka sanya masa Ba-Ya-Ji-Da, wato ba ya jin Hausa a da.

Masana tarihi sun ce Bayajidda ne ya kashe wata macijiya a rijiyar nan ta Kusugu da ke Daura. Macijiyar a wancan lokacin ta addabi mutanen garin inda take hana su ɗibar ruwa. Sau ɗaya kacal suke samun damar jan ruwa a mako wato ranar Juma’a, saboda yadda wannan macijiya ta yi ƙaƙa-gida a wannan rijiya.

Duk da gargaɗin da aka yi masa, Bayajidda ya yi ƙoƙarin ɗibar ruwa a ranar Alhamis wato ranar da ba a ɗibar ruwa, a nan ne macijiya ta harzuƙo ta so hallaka shi, amma sai ya fille ma ta kai da takobinsa. Daga baya ne sarauniya Daurama ta amince ta aure shi saboda bajintar da ya nuna.

An ce Bayajidda na da ’ya’ya uku, na farko shi ne Biram wanda ya haifa da ’yar sarkin daular Borno, sai kuma Bawo wanda ya haifa da Sarauniya Daurama na ukun kuma ya haife shi ne da wata kwarkwara.

Bawo ya haifi ’ya’ya shida kuma tare da kawunsu wato Biram su ne suka mulki garuruwan da ake kira Hausa bakwai wanda suka haɗa da Daura da Kano da Katsina da Zariya da Gobir da Rano da kuma Biram.

To sai dai farfesa Abdallah Uba Adamu, shugaban jami’ar koyo daga gida ta Nijeriya, wanda masanin harshe da al’adun Hausawa ne ya ce, “alaƙanta Hausawa da Bayajidda shafcin gizo ne.”

Ya kuma ce, “duk mutumin da ba shi da alaƙa da garuruwa guda bakwai da ke arewacin Nijeriya, to ba Bahaushe ba ne. Sai dai a kira shi mai magana da yaren Hausa.”

Garuruwan dai su ne birnin Kano da Katsina da Daura da Zazzau da Rano da Gobir da kuma Biram.

Farfesa Abdallah ya kuma yi watsi da batun da wasu manazarta ke faɗi cewa Hausa yare ne ba ƙabila ba, a inda ya ce, “Hausawa na da daulolinsu.”

To, sai dai martanin da farfesa Tijjani Muhammad Naniya na jami’ar Bayero ya yi game da waɗannan kalamai na Farfesa Abdallah Uba, shi ne babu wani abu a duniya da ake zancensa ba tare da babu shi ba.

“Duk abin da ka ga ana maganarsa to akwai shi, zan yarda idan aka ce ƙila an yi ƙarin gishiri, ko kuma an yi wani kuskure a ciki, amma ba wai ace babu shi dungurungum ba.”

Wane ne Bahaushe?
Na tabbatar ƙasar Hausa ta riga Bahaushe zama a sararin duniya, amma duk da haka da ba Bahaushe ya fara sauka a kanta ba da ƙasar wasu ce ta daban. Bahaushe dole ya kasance a wajen iyaye uba da kaka duk Hausawa ne. A same shi yana bugun ƙirjin zama Bahaushe mai iƙirari ko alfahari da wata zuriya daga cikin zuriyar Hausawa. Samunsa cikin ƙasar Hausa ba tilas ba ne, kamar yadda addini da sana’a ba su cikin shika-shikan tantance shi.

Mece ce Hausa?
A nan ma, masana ba su yi ƙamfar fito da ra’ayoyinsu ba, domin lalubo tabbatacciyar ma’anar harshen Hausa ba. A wata fassara su kira ƙabilarsu da sunan. A wani zubin su kira fasaharsu da suke da ita da sunan. A fagen yaƙi, waɗansu kan kira qasar Hausa da ke hannun Fulani ‘Hausa’ ga su nan dai. Manazarta Hausa a wajen ƙasar Hausa suna bai wa kalmar ‘Hausa’ ma’anoni mabambanta. Waɗansu daga cikinsu su suka haifar da ruɗanin da ake ciki a yau.

Matsayin Harshen Hausa a cikin Afirka:
Wannan wata dama ce za mu rairaye ra’ayoyin da ke kwatanta Hausa da Bantu, da kuma masu ganin Hausa ba ta da wani tarihin asali da ma za ta tsaya a yi nazari. Haka kuma, za mu gano tsawo da faɗin harshen Hausa a duniyar da Bahaushe ya zauna da waɗanda suka yi tarayya a yaƙin neman jama’a da su da waɗanda ya cinye da waɗanda suka shige masa hanci ya kasa fyacewa.

Hausawa su ne mafi yawan ƙabila, kuma mafi yawan bazuwa a Afirka. Akwai Hausawa da waɗanda Hausa ta rikiɗe (Hausantar) a manyan birane na Afirka ta Yamma da Afirka ta Arewa. Mafi yawansu (Hausawa) sun mamaye Arewa-maso Gabashin Jamhuriyar Nijar da Benuwai.

Babu wai, al’ummar da ta samu wannan shaidar tana kasancewa kan takarda a ƙididdirgar al’ummomin Afirka da duniya ba a yi musu adalci ba idan aka ƙi zama a tantance asalinsu. A harsunan duniya, Hausa ba ƙyalle ba ce, ko cikin gida Afirka. Mamaye duniyar Afirka da Hausawa suka yi da masu magana da harshen Hausa suka yi, shi ya zama wata allura ta zaburar da mu tono ruwa domin Hausawa sun ce, yana ƙasa sai ga wanda bai tona ba.

Yaren Hausa na daga cikin manyan yarukan nahiyar Afrika. Har yanzu ba a samu takamaiman tarihin asalin yaren Hausa ba, masana da yawa sun yi ƙoƙari wajen kawo tarihin asalin yaren Hausa da Hausawa. Wani bincike ya nuna cewar akwai kimanin mutum miliyan 38 da ke yaren Hausa a faɗin duniya. Akwai Hausawa a ƙasashen duniya da dama, kuma bincike ya nuna sun yi hijira ne daga ƙasashen Afrika ya zuwa sauran ƙasashen nahiyoyin duniya.

Al’adun Hausawa:
Farfesa Tijjani Naniya ya bayyana cewa, Hausawa mutane ne musu tsananin riqon al’adunsu na gargajiya, musamman wajen tufafi da abinci da al’amuran da suka shafi aure ko haihuwa ko mutuwa da sha’anin mu’amala tsakanin dangi da abokai da shugabanni da sauransu, da kuma al’amuran sana’a ko kasuwanci ko neman ilmi.

Tun daga zuwan Turawa har yau, Hausawa suna cikin al’ummomin da ba su saki tufafinsu na gargajiya sun ari na baki ba.

Galibin adon namiji a Hausa ba ya wuce riga da wando musamman tsala, da takalmi faɗe ko ƙafa-ciki, da hula kube, ko dankwara, ko dara. Idan kuma saraki ne ko malami ko dattijo, ya kan sa rawani.

Adon mata kuwa, zane ne da gyauton yafawa, wato gyale da kallabi da taguwa da ’yan kunne da duwatsun wuya wato tsakiya. Yawancin abincin Hausawa kuwa, ana yin sa da gero ko dawa.

Sai kuma sauran abubuwan haɗawa, da na marmari, kamar su wake da shinkafa da alƙama da kayan rafi da sauransu. Yawancin Hausawa Musulmi ne saboda haka yawancin al’adunsu da suka shafi aure da haihuwa da mutuwa duk sun ta’allaƙa ne da wannan addni.

Haka kuma wajen mu’amala da iyaye ko dangi ko abokai ko shugabanni ko makwabta ko wanin waɗannan, yawanci na Musulunci ne. Haka nan sha’anin sana’a da kasuwanci da neman ilmi duk a jikin Musulunci suka rataya.

Da can sana’a da kusuwanci da neman ilmi suna bin gado ne, wato kowa yana bin wadda ya gada kaka da kakanni. Kuma idan mai sana’a ya shiga baƙon gari zai je ya sauka a gidan abokan sana’arsa ne.

Idan ma koyo ya zo yi, zai je gidan masu sana’ar gidansu ne saboda haka kusan kowace sana’a akwai sarkinta da makaɗanta da mawaƙanta, kai har ma da wasu al’adu na masu yinta da suka sha bamban da na sauran jama’a.

Hausawa na da sana’o’i da daman na gargajiya da suke yi tun fil azal, suna da tarin yawa, amma ga wasu daga cikinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *