Beijing 2022: Yawan ‘yan wasa mata sun kafa tarihi

Daga CRI HAUSA

Tashar yanar gizo ta jaridar Neues Deutschland ta ƙasar Jamus, ta ruwaito a kwanan baya cewa, an kafa tarihi a yawan ‘yan wasa mata da suka shiga gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta shekarar 2022. A cikin dukkan ‘yan wasa kimanin 2900, kaso 45 cikin ɗari mata ne. Sakamakon gasar da ke gudana yanzu, ya sa ana ƙara samun daidaito a tsakanin mata da maza a gasar wasannin Olympics.

A yayin gasar da aka yi a Tokyo na ƙasar Japan, yan wasa mata na ƙasar Sin sun fi maza na ƙasar yawa da fiye da ninki biyu, yayin da gasar da ke gudana a Beijing, aka samu yan wasa mata 87 da maza 89 cikin ƙungiyar yan wasan ƙasar Sin.

Kamfanin dillancin labaru na Agence France-Presse (AFP) ya labarta cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, ta fi samun daidaiton adadi tsakanin maza da mata a tarihi. A ganin yan wasa, ƙara yin takara tsakanin ƙungiya mai haɗakar mata da maza na da maana sosai, lamarin da ya taimaka wajen kyautata matsayin wasannin mata.