Bello Turji ya yi layar zana yayin da sojoji suka kashe kwamandojin ƴan bindiga, inji NAF

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Lahadi ne Rundunar sojojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta ce kwamandojin ƴan bindiga da dama ne suka rasa rayukansu a wani hari ta sama da jami’anta suka kai wa maɓoyarsu a Jihar Zamfara.

Daraktan yaɗa labarai na NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa ya bayyana hakan a wata sanarwa inda ya ce jami’ansu sun kai farmakin ne da haɗin-gwiwar sojojin ƙasa wanda ya raunata wasu da dama daga cikin ƴan ta’addar.

Ya ce wani rahoton sirri ya tabbatar da cewa ƴan bindigar mambobin dabar sanannen jagoransu ne, Kachalla Bello Turji, waɗanda sun fuskanci mummunar iftila’i a yayin farmakin.

Saidai, Daraktan ya ce duk da haka, ba a san takamaiman wajen da Bello Turji ya ke ba.

Ya ƙara da cewa jami’an sun gudanar da atisayen ne ƙarƙashin shirin tawagar FANSAN YAMMA wanda ke cigaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tsaro a shiyyar Arewa-maso-Yamma.

Jami’in ya bayyana cewa an gudanar da atisayen ne bayan bincike na sirri da kuma kimtsi da jami’an suka yi na tabbatar da nasara.

An dai samu nasarar kashe ƴan bindigar ne a lokacin da suka yi yunƙurin tserewa wanda hakan ya bai wa sojojin damar hallaka ƙarin wasu da dama daga cikin su.

Al’umma da dama sun bayyana farin cikinsu game hoɓɓasa da jami’an suka yi wanda ya taimaka wajen ceto da dama daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su tare da miƙa su ga iyalansu.

Har’ilayau, rundunar ta bayyana aniyarta na cigaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen kowane irin ta’addanci a Nijeriya don dawo da zaman lafiya da samun nasarori ga ƙasar da al’ummarta.