Bello ya musanta zargin naɗa shi shugabancin wuci-gadi na APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa tun da sanyin safiyar Litinin jami’an ‘Yan Sanda suka mamaye hanyoyin dake kai mutane hedikwatar Jam’iyyar APC da ke Abuja, wanda ke nuna alamar barazanar tsaro, yayin da kafofin yaɗa labarai suka dinga bayyana cewar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da buƙatar maye gurbin Mai Mala Buni daga muƙamin sa domin bai wa Gwamna Abubakar Sani Bello damar jagorancin jam’iyyar a matsayin wucin gadi, duk da yake babu wata sanarwa a hukumance dangane da haka.

Wannan ya sa Sakataren jam’iyyar na riƙo, John James Akpanudoede fitar da sanarwa inda yake musanta sauke Bunin, abinda ya bayyana shi a matsayin labaran ƙarya.

Amma kuma daga bisani sai aka ga Gwamna Bello ya isa hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, inda ya gudanar da taro tare da wasu shugabannin ta dake shirya yadda za a gudanar da taron jam’iyyar na ƙasa da suka haɗa da gwamnonin wasu jihohi da kuma wasu shugabannin jam’iyyar.

Bayan kammala taron, Bello ya shaida wa manema labarai cewar sun tattauna batun ci gaban da aka samu dangane da shirin taron jam’iyyar da zai gudana ranar 26 ga watan nan.

Kana, a wani faifan bidiyo da ke yawo a yanar gizo, ɗan jarida ya yi wa Gwamna Sani Bello tambaya akan maganganun da ke yawo dangane da naɗa shi shugaban jam’iyyar na wucin gadi, inda Bello ya bayyana cewar labari ne na ƙanzon kurege.

Sai dai tun shigar shi sakatariyar jam’iyyar an jiyo muryar wasu muƙarraban sa suna taya sa murna tare da kiran sa ‘Shugaban Jam’iyya’, wanda hakan ke nuni da cewa akwai magana a ƙasa.

Ya zuwa wannan lokaci babu wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya tafi Landan domin kula da lafiyar sa ko kuma ɓangaren jagoran jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu dangane da abinda ke faruwa a ofishin jam’iyyar.