Bello ya ziyarci sansanin jami’an tsaro don ƙarfafa musu gwiwa

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya yaba wa rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaron da aka jibge a ƙwauyen Kundu da ke yankin ƙaramar hukumar Rafi a jihar bisa ƙoƙarin da suka yi wajen daƙile harin ‘yan bindiga a yankin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan bindigar da dama da kuma jami’an tsaro biyu.

Bello ya yi wannan yabo ne a lokacin da ya ziyarci jami’an tsaron a sansaninsu domin gane wa idanunsa irin ƙoƙarin da suke yi da kuma ƙarfafa musu gwiwa wajen dawo da lumana a yankin.

Sanarwar da Sakatariyar Labarai ta Gwamnan, Mary Noe-Berje, ta fitar a Lahadi ta nuna gamsuwar gwanan bisa aiki tukuru da jami’an ke yi tare da yin alƙawarin tallafa wa iyalan jami’an da suka rasa ransu yayin artabun.

Bello ya ƙara da cewa, Jihar Neja ta samu kwanciyar hankali a ‘yan kwanakin nan sakamakon ƙoƙarin da jami’an tsaron ke ci gaba da nunawa a fagen yaƙi da harkokin ‘yan ta’adda a jihar.

Ya ce duk da dai babu inda ake da tabbacin tsaro ɗari bisa ɗari amma cewa, za su yi bakin ƙoƙarinsu wajen dawo da cikakken zaman lafiya a faɗin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *