BIDIYO: An gano tulin Katin Zaɓe ɓoye a dajin Anambra

Daga WAKILINMU

Yayin da ya rage kwana uku kafin zaɓen 2023, an gano tulin Katin Zaɓe da aka ɓoye a daji a yankin Ƙaramar Hukumar Nnewi ta Arewa a Jihar Nnewi Anambra.

Wani faifan bidiyon da aka yaɗa ya nuna wasu mahauta biyu suka gano katin a cikin jaka a dajin ƙauyen Akamili da ke yankin a ranar Talata inda suka ɗauka suka kai tashar Authority FM da ke yankin.

Bayanai sun ce galibin katin na jama’ar yankin Ƙaramar Hukumar Nnewi ta Arewa ne.

Kuma cewa, an kwashi katin an kai an miƙa wa shugabannin yankin.

Da aka nemi jin ta bakinsa, shugaban gidan rediyon, Charles Ede, ya tabbatar da faruwar hakan.

Ya ce, “Ba na bakin aiki lokacin da lamarin ya faru, amma wani ma’aikacinmu ya karɓi mafarautan da suka gano katin.

Ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin mai magana da yawun INEC a jihar, Dr Kingsley Agu, ya ci tura kasancewar ya ƙi ɗaga kiran waya da aka yi masa.

A hannu guda, Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Anambra, Mr Tochukwu Ikenga, ya ce, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr Echeng Echeng, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan faifan bidiyon don gano gaskiyar lamari, wataƙila kuma a cafke du wani mai hannu a badaƙalar.

Kalli Bidiyon:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *