BIDIYO: Fasto ya yanke jiki ya faɗi a filin jirgin sama a Ribas

Daga BASHIR ISAH

Wani faifan bidiyo da aka yaɗa a kafafe daban-daban ya nuna yadda mu’assasin cocin Omega Power Ministries (OPM), mai suna Apostle Chibuzor Gift Chinyere, ya yanke jiki ya faɗi ranar Juma’a a filin jirgin saman da ke Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Majiyarmu ta ce wannan na zuwa ne bayan da wanda lamarin ya shafa ya sanar cewa ba ya jin daɗin jikinsa, kuma yana buƙatar addu’a.

Bayan faruwar lamarin, daga bisani an ga cocin nasa ya yaɗa wani hoton Faston kan cewa yana asibiti yana ci gaba da karɓar magani.

Haka shi ma Fasto ɗin, ya wallafa hotonsa da yake kan gadon asibiti a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

Ga bidiyon: